NNPP ta fara ratsa wasu jihohi, ta sha alwashin karbe mulki daga hannun APC da PDP

NNPP ta fara ratsa wasu jihohi, ta sha alwashin karbe mulki daga hannun APC da PDP

  • Jam’iyyar hamayya ta New Nigeria People’s Party ta na gudanar da zaben shugabanninta a yanzu
  • An shirya zabuka a mazabu da kananan hukumomi a jihohin kasar nan musamman a yankin Arewa
  • NNPP ta fitar da jerin sababbin shugabannin a reshen jihohin Nasarawa, Ogun, Katsina da sauransu

Jaridar Punch ta kawo rahoto cewa jam’iyyar NNPP ta fito da sababbin shugabanni a jihar Nasarawa wadanda za su jagoranci jam’iyyar har zuwa 2026.

An fito da shugabannin ne ta hanyar maslaha a duka kananan hukumomi 13 da ke Nasarawa. Sababbin shugabannin sun ce za su karbe shugabanci a 2023.

Sabon shugaban NNPP na jihar ta Nasarawa, Sidi Bako ya shaidawa manema labarai cewa a shirye suke su kawo romon damukaradiyya ga jama’a a badi.

“Ba mu goyon bayan siyasar uban gida da kama-karya na kakaba ‘yan takara saboda ba mu son duk wani mara farin jini a wajen jama’a.”

Kara karanta wannan

Gwamna Buni ga masu sukar APC: Taron gangami ne a gabanmu, ba ta kowa muke ba

“NNPC jam’iyya ce da ke ba al’umma dama su zabi shugabannin da suke so.” - Sidi Bako.

An yi zabe a Katsina

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa haka lamarin yake a Katsina inda aka rantsar da sababbin shugabannin wannan jam’iyya mai taken ‘mai kayan marmari.'

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

'Yan NNPP
Zaben shugabannin NNPP Hoto: @Salisuyahayahototo
Asali: Facebook

Tsohon Sanatan Katsina, Abdu Umar ‘Yandoma a shafinsa na Facebook ya tabbatar da cewa an nada Alhaji Gambo Salisu a matsayin sabon shugaban NNPP.

Alhaji Gambo Salisu, Hadi Maidawa Malumfashi, Dauda kurfi, Dauda kurfi, Abdulaziz Musawa, Hajiya Guye Daura su na cikin shugabanni na reshen Katsina.

Kafin nan, daya daga cikin jiga-jigan tafiyar NNPP a Arewa maso yamma, Aminu Ibrahim Ringim ya tabbatar da cewa NNPC ta shirya zaben ta a jihar Jigawa.

An ji cewa an gudanar zaben shugabannin jam’iyyar ne a filin wasa na Ghaladanci da ke garin Dutse kamar yadda Malam Ringim ya bayyana a Facebook.

Kara karanta wannan

Kan gwamnoni da jiga-jigai ya yi kwari, sun shirya yakar ‘Yan takarar Buhari a zaben APC

Wani rahoto ya nuna NNPC ta zabi sababbin shugabanni a jihar Ogun inda jam’iyyar ta koma hannun Oginni Olaposi da wasu mutane 34 da za su taya shi riko.

A jihohin Kaduna da Kano, duk an yi irin wannan zabe domin NNPP ta shiryawa 2023. Umar Haruna Doguwa ne ya zama sabon shugaban NNPP a jihar Kano.

Rikicin APC a Kano

A baya kun ji cewa ana shari’a tsakanin bangaren Ibrahim Shekarau da su Barau Jibrin da tsagin Gwamnatin Ganduje inda har rikicin ya kai gaban kotun koli.

Hakan zai iya jawo a samu manyan bangarori uku da za su yi takara a jihar Kano a zabe mai zuwa. Za a iya samun 'Yan APC, PDP da kuma jam'iyyar NNPP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel