Taron gangamin APC: Jerin kujerun shugabancin jam'iyyar APC 23 da ya kamata ku sani

Taron gangamin APC: Jerin kujerun shugabancin jam'iyyar APC 23 da ya kamata ku sani

Komai ya kammalu domin gudanar da babban gangamin taron jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a ranar Asabar, 26 ga watan Maris.

Hakan na zuwa ne duk da tarin matsalolin da jam’iyyar mai mulki ke fuskanta, musamman na kwamitin riko da Gwamna Mai Mala Bunin a jihar Yobe ke jagoranta.

Taron gangamin APC: Jerin kujerun shugabancin jam'iyyar APC 23 da ya kamata ku sani
Taron gangamin APC: Jerin kujerun shugabancin jam'iyyar APC 23 da ya kamata ku sani Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

A wannan rahoton, Legit Hausa ta tattaro dukka mukaman da za a yi takara kansu a babban taron jam’iyyar. Sai dai, domin ganin an yi babban taron cikin nasara, shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnonin APC sun cimma matsaya na aiki wajen ganin an zabi yan takara na bai daya.

1. Shugaban jam'iyya na kasa

2. Sakataren jam’iyya na kasa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Yadda mutane kusan 200 za su goge raini wajen neman mukamai 22 a Jam’iyyar APC

3. Mataimakin sakataren jam’iyya na kasa

4. Mataimakan shugaban jam’iyya na kasa daga shiyoyyi shida

5. Sakataren Tsare-Tsaren jam'iyya na kasa

6. Mai ba jam'iyya shawara kan harkokin shari'a na kasa

7. Sakataren kudin jam’iyya na kasa

8. Sakataren kula da jin dadin jam’iyya na kasa

9. Ma’ajin jam’iyya na kasa

10. Sakataren yada labarai na jam'iyya na kasa

11. Mai binciken kudi na jam'iyya na kasa

12. Shugabar Matan jam'iyya na kasa

13. Shugaban matasan jam’iyya na kasa

14. Shugaban nakasassun jam’iyya

14. Mataimakin sakataren kudin jam’iyya na kasa

15. Mataimakin mai ba jam'iyya shawara kan harkokin shari'a na kasa

16. Mataimakin ma’ajin jam’iyya na kasa

17. Mataimakin sakataren kula da jin dadin jam’iyya na kasa

18. Mataimakin sakataren yada labarai na jam'iyya na kasa

19. Mataimakin mai binciken kudi na jam'iyya na kasa

20. Mataimakiyar shugabar Matan jam'iyya na kasa

21. Mataimakin shugaban matasan jam’iyya na kasa

Kara karanta wannan

Kan gwamnoni da jiga-jigai ya yi kwari, sun shirya yakar ‘Yan takarar Buhari a zaben APC

22. Sakatarorin shiyya daga yankuna shida

23. Shugabannin matasan shiyya a shiyoyi shida

Fayemi ya yi watsi da batun goyon bayan yan takarar da Buhari ke so

A gefe guda, Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti ya karyata batun goyon bayan yan takarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya lamunce mawa gabannin babban taron jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Daily Trust ta rahoto.

Da yake magana a taron tattaunawa kan manufofi da cibiyar ci gaban damokradiyya wato Centre for Democracy and Development (CDD), ta shirya a ranar Alhamis, 24 ga watan Maris, Fayemi ya karyata goyon bayan yan takarar da shugaban kasa yake goyon baya.

Furucin Fayemi zai ba mutane da dama mamaki domin yana daga cikin gwamnonin APC da suka tabbatar da tsarin cimma matsaya daya bayan ganawarsu da shugaba Buhari a daren ranar Laraba, 23 ga watan Maris.

Asali: Legit.ng

Online view pixel