Babban taron APC: Bidiyon shugaba Buhari yayin da ya isa wajen rantsar da shugabannin APC na kasa

Babban taron APC: Bidiyon shugaba Buhari yayin da ya isa wajen rantsar da shugabannin APC na kasa

  • An rantsar da kwamitin shugabancin APC na kasa karkashin jagorancin Sanata Abdullahi Adamu
  • An rantsar da Adamu da sauran mambobin kwamitin a ranar Lahadi, 26 ga watan Maris, yayin gangamin taron jam’iyyar mai mulki a Eagles Square da ke Abuja
  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari, mataimakin shugaban kasa da sauran manyan shugabannin jam’iyar sun halarci taron

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa filin taro na Eagle Square da ke Abuja domin rantsar da sabbin shugabannin jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

A ranar Asabar, 26 ne aka zabi sabbin shugabannin jam’iyyar mai mulki a wajen babban gangamin taron jam’iyyar.

Babban taron APC: Bidiyon shugaba Buhari yayin da ya isa wajen rantsar da shugabannin APC na kasa
Babban taron APC: Bidiyon shugaba Buhari yayin da ya isa wajen rantsar da shugabannin APC na kasa Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta rahoto cewa an rantsar da sabbin mambobin kwamitin aiki na jam'iyyar APC na kasa a Abuja.

An tattaro cewa mambobin kwamitin NWC karkashin jagorancin Sanata Abdullahi Adamu sun yi rantsuwar kama aiki wanda ya samu halartan shugaba Buhari, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da shugabanni da mambobin jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Gangamin taron APC: Buhari ya aika gagarumin sako ga Adamu, Omisore da sauran zababbun shugabanni

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban kwamitin babban gangamin taron, Gwamna Badaru Abubakar ya ce biyar daga cikin mukamai 36 na NWC ne kawai akayi takara yayin da aka zabi sauran ta hanyar yarjejeniya.

Ga bidiyon isowar shugaban kasar wanda jaridar Punch ta wallafa:

Ga hotunan taron wanda hadimin shugaban kasa, Buhari Sallau ya wallafa a shafinsa na Facebook:

Gangamin taron APC: Buhari ya aika gagarumin sako ga Adamu, Omisore da sauran zababbun shugabanni

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bukaci sabuwar zababbiyar uwar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) karkashin jagorancin Sanata Adamu Abdullahi da ta tabbatar da ganin cewa wadanda suka cancanta ne suka mallaki tikitin jam’iyyar a zaben 2023.

Buhari ya bukaci sabbin shugabannin da su inganta damokradiyyar cikin gida da daidaito sannan su tabbatar da ganin cewa ba’a yi cuwa-cuwa ba a zaben fidda gwanin jam’iyyar gabannin zaben 2023, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Yanzu adadin mambobin jam'iyyar APC milyan 41 a Najeriya, Mai Mala Buni

Da yake jawabi a babban taron gangamin jam’iyyar da aka yi a ranar Asabar, a Eagle Square Abuja, shugaban kasar ya kuma yi kira ga mambobin APC da su ci gaba da kasancewa a hade da karfi sannan su marawa sabon shugabancin jam’iyyar baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel