'Yan Ta'adda Fiye Da 40,000 Sun Miƙa Wuya Da Sojojin Najeriya, DHQ

'Yan Ta'adda Fiye Da 40,000 Sun Miƙa Wuya Da Sojojin Najeriya, DHQ

  • Hedkwatar tsaro ta Najeriya, DHQ, ta yan ta'adda da iyalansu kimanin guda 47,975 ne suka mika wuya daga Satumban 2021 zuwa yanzu
  • Manjo Janar Bernard Onyeuko, kakakin na DHQ ne ya bayyana hakan yayin jawabin nasarorin da ta samu cikin wannan lokacin
  • Manjo Onyeuko ya lissafo hare-hare daban-daban na sama da kasa da dakarun sojojin suka kai da kuma makamai da mutane da suka kama

Hedkwatar tsaro ta Najeriya, DHQ, ta ce yan ta'adda da iyalansu guda 47,975 na kawo yanzu suka mika kai ga dakarun sojoji na Operation Hadin Kai a arewa maso gabas daga Satumban 2021 zuwa yanzu, rahoton Premium Times.

Direktan sashi watsa labarai, Manjo Janar Bernard Onyeuko, ne ya bayyana hakan yayin da ya ke bada jawabi kan ayyukar sojojin daga ranar 10 ga watan Maris zuwa 24 ga watan Maris, a ranar Alhamis a Abuja.

Kara karanta wannan

Da duminsa: An yi artabu tsakanin Soji da yan Boko Haram a Sambisa, Soji sun yi nasara

'Yan Ta'adda Fiye Da 40,000 Sun Miƙa Wuya Da Sojojin Najeriya, DHQ
'Yan Ta'adda Fiye Da 40,000 Sun Miƙa Wuya Da Sojojin Najeriya, In ji DHQ. Hoto: DHQ
Asali: Facebook

Mr Onyeuko ya ce nasarorin da sojojin suka samu cikin lokacin ya hada da kashe yan ta'adda 17, kama 35, kwato AK-47 34, bindigan mafarauta biyar da bindigu kirar Najeriya guda tara.

Ya kuma ce sojojin sun kwato shanu 270 da aka sace, babura uku da kekuna 13 da yan ta'addan ke amfani da shi na zirga-zirga.

A cewarsa, yan kungiyar ISWAP da Boko Haram 7000 daga yankuna daban-daban sun mika wuya, sojojin sun ceto farar hula 27 cikin makonni biyu da suka shude.

"An yi wa yan ta'addan da suka mika wuya tambayoyi, yayin da fararen hula da kayayyakin da aka kwato an mika su ga hukumomin da suka dace don daukan mataki na gaba," in ji shi.

Nasarorin Operation Hadarin Daji

Kara karanta wannan

Mayakan ISWAP 7,000 sun ajiye makamai tare da mika wuya a mako 1, Rundunar soji

A wani hari Operation Hadarin Daji na sojojin sama suka kaddamar a ranar 14 ga watan Marisa kauyen Unguwar Adam a karamar hukumar Danmusa a Jihar Katsina, an kashe yan ta'adda fiye da 27, a cewar Mr Onyeuko.

Ya ce an kai harin ne bayan samun bayanin sirri cewa yan ta'adda fiye da 50 za su gana da manyan kwamandojinsu a wurin, kamar yadda Premium Times ta rahoto.

Ya karada cewa wani Malam Sule, dan uwan hatsabibin shugaban yan bindiga Lalbi Ginshima, yana cikin wadanda aka kashe.

Kakakin sojojin ya kuma ce an kashe wasu yan ta'addan a harin da sojojin sama suka kai mabuyarsu a Magaba, Jihar Kaduna.

Ya kuma ce sojojin sun kashe yan bindiga takwas, sun kama bakwai, sun ceto mutum 56 sun kuma kwato makamai da wasu kayayyakin.

Nasarorin Dakarun Operation Safe Haven

A Operation Safe Haven Mr Onyeka ya ce sojoji sun kwato karafen layin dogo da aka sace, motocci uku, bas J5 guda daya da AK47 biyu da harsashi yayin ayyukansu.

Kara karanta wannan

Sojan Najeriya da ya sha Kwayar Maye ya bindige mutane har Lahira a Borno

Ya ce dakarun sojojin sun kuma ceto fararen hula, sun kashe yan bindiga biyu, sun kama 19, daga bisani suka mika su ga hukumomin da suka dace.

Nasarorin Operation Whirl Stroke

A Operation Whirl Stroke, sojojin sun kashe a kalla yan bindiga 10, sun kama biyar sun kwato motocci daban-daban da makamai.

A cewarsa sojojin suna cigaba da ragargazan yan ta'addan, yan fashin daji da sauran makiyan kasa.

"A yayin da aka samu zaman lafiya a wasu yankunan, an samu hare-hare a wasu wuraren a lokacin," in ji shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel