Da duminsa: An yi artabu tsakanin Soji da yan Boko Haram a Sambisa, Soji sun yi nasara

Da duminsa: An yi artabu tsakanin Soji da yan Boko Haram a Sambisa, Soji sun yi nasara

  • Hukumar Sojin Najeriya ta saki hotuna da bidiyo biyo bayan artabun da ya gudana tsakaninsu da yan Boko Haram
  • Artabun ya auku ne a Camp Zairo, dajin Sambisa dake cikin jihar Borno, Arewa maso gabashin Najeriya
  • A baya, dakarun sojin sun kwace Camp Zairo na dajin Sambisa hannun yan ta'addan Boko Haram

Borno - Hukumar Sojin Najeriya ta sanar da gagarumin nasarar da ta samu kan yan ta'addan ISWAP/Boko Haram a garin Ukuba da Camp Zairo dake dajin Sambia, jihar Borno.

Hukumar, a jawabin, hotuna da bidiyon da ta saki ranar Juma'a, 25 ga watan Maris tace ta hallaka dimbin yan ta'addan kuma an ragargaza makamansu.

A cewarta:

"Mun sake samun nasara a hare-haren kawar da yan ta'adda da mukeyi yayinda rundunar Operation Desert Sanity suka ragargaji yan ta'addan ISAWP/Boko Haram a Ukuba/Cam Zairo dake dajin Sambisa , jihar Borno.

Kara karanta wannan

'Yan Ta'adda Fiye Da 40,000 Sun Miƙa Wuya Da Sojojin Najeriya, DHQ

"An kashe dinbim yan ta'addan kuma an kwato kayayyaki da makamai."

Kalli hotunan da bidiyon:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sambisa
Da duminsa: An yi artabu tsakanin Soji da yan Boko Haram a Sambisa, Soji sun yi nasara Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

'Yan Ta'adda Fiye Da 40,000 Sun Miƙa Wuya ga Sojojin Najeriya, DHQ

Hedkwatar tsaro ta Najeriya, DHQ, ta ce yan ta'adda da iyalansu guda 47,975 na kawo yanzu suka mika kai ga dakarun sojoji na Operation Hadin Kai a arewa maso gabas daga Satumban 2021 zuwa yanzu.

Direktan sashi watsa labarai, Manjo Janar Bernard Onyeuko, ne ya bayyana hakan yayin da ya ke bada jawabi kan ayyukar sojojin dasga ranar 10 ga watan Maris zuwa 24 ga watan Maris, a ranar Alhamis a Abuja.

Mr Onyeuko ya ce nasarorin da sojojin suka samu cikin lokacin ya hada da kashe yan ta'adda 17, kama 35, kwato AK-47 34, bindigan mafarauta biyar da bindigu kirar Najeriya guda tara.

Kara karanta wannan

Bayan zabtare albashin masu mukamai, hotunan shugaban kasar Ghana a Aso Rock sun bayyana

Ya kuma ce sojojin sun kwato shanu 270 da aka sace, babura uku da kekuna 13 da yan ta'addan ke amfani da shi na zirga-zirga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel