Wani Soja da Kwaya ta ɗibe shi ya bindige mutanen gari har Lahira ba zato a Borno

Wani Soja da Kwaya ta ɗibe shi ya bindige mutanen gari har Lahira ba zato a Borno

  • Wani Sojan Najeriya da ake zaton yana cikin kwayoyin Maye ya harbe mutum uku har lahira ranar Laraba a jihar Borno
  • Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa yanzu haka gawarwakin na kwance a garin Mafa, kuma wasu kusan 13 sun jikkata
  • Rundunar sojin Najeriya ba tace komai ba game da lamarin, amma wasu bayanai sun ce an kama Sojan da ya aikata kisan

Borno - Wani Soja a hukumar sojojin Najeriya dake aiki a rundunar operation Hadin Kai ya bindige fararen hula uku har Lahira ranar Laraba a jihar Borno, kamar yadda The Cable ta tataro.

Sojan wanda ke aiki a karamar hukumar Mafa ta jihar Borno, bayanai sun nuna cewa Kwayoyin dake sa maye ne suka rinjaye shi ya aikata wannan ɗanyen aikin.

Sojan Najeriya ya yi shirin aiki.
Wani Soja da Kwaya ta ɗibe shi ya bindige mutanen gari har Lahira ba zato a Borno Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

A cewar wata majiya, ba zato ba tsammani Sojan ya buɗe wuta kan mazauna garin Mafa, uku suka mutu, wasu na kwance a Asibiti.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun yi awon gaba da sabuwar Amarya, sun sha alwashin sai an biya N10m

Wani shaidan gani da ido ya ce:

"Yanzu haka gawarwakin mutum ukun da abun ya shafa na kwance a garin Mafa yayin da wasu da dama suka samu raunin harbin bindiga."

Rahoto ya nuna cewa kusan mutum 13 ke kwance a Asibiti biyo bayan raunukan harbin bindiga da suka samu a tsautsayin da ya rutsa da su.

Wane matakin rundunar sojojin Najeriya ta ɗauka?

Yayin da aka tuntuɓi kakakin rundunar sojin ƙasa ta Najeriya, Onyema Nwachukwu, domin jin matakin da suka ɗauka ba'a same shi ba.

Sai dai wasu bayanai sun nuna cewa tuni hukumomin soji suka kwace makaman dake tare da Sojan kuma suka kama shi.

Wannan ba shi ne na farko da aka samu sojan dake aiki a arewa ta tsakiya ya buɗe wa mutane wuta ba ko kuma abokanan aikinsa na rundunar soji.

Kara karanta wannan

Dan a mutun siyasa ya mutu yana tsaka da murnar sauya shekar Uban Gidansa daga APC zuwa PDP

A 2017, Kotu ta yanke wa wani Soja hukuncin kisa bisa zargin halaka wasu fararen hula har mutum biyar a jihar Borno.

Haka nan kuma a shekarar 2020, wani Soja ya sheƙe na gaba da shi saboda kawai ya hana shi izinin zuwa gida ya duba iyalansa.

A wani labarin na daban kuma Yan bindiga sun sako mutum 75 da suka sace a harin jihar Zamfara, sun faɗi yadda suka yi da wata yarinya

Yan ta'adda sun amince sun sako mutum 75 da suka yi garkuwa da su a kauyen Yar Katsina, karamar hukumar Bungudu a Zamfara.

Wani mazaunin ƙauyen ya bayyana cewa yan bindigan sun rike wata yarinya yar shekara shida saboda ɗayansu ya maida ta ɗiyarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel