Masu garkuwa da mutane sun halaka dan kasuwa, sun sace matarsa da yaransa

Masu garkuwa da mutane sun halaka dan kasuwa, sun sace matarsa da yaransa

  • Wasu masu garkuwa da mutane sun halaka fitaccen mai saida shanu, tare da yin garkuwa da matarsa da ƴaƴansa maza a Jalingo
  • An tattaro yadda aka kai wa Alhaji Gidado Hassan, wanda ke shugabantar kasuwancin raguna a Jalingo farmaki a gidansa dake ƙauyen Audi, misalin ƙarfe 2:00 na dare
  • Haka zalika, an birne marigayin a babbar maƙabartar Jika Da Dari misalin karfe 9:30 na safiyar Alhamis

Taraba - A ranar Laraba, wasu masu garkuwa da mutane sun halaka fitaccen mai saida shanu, tare da yin garkuwa da matarsa da ƴaƴansa maza a Jalingo, babban birnin jihar Taraba.

An tattaro yadda aka kai wa dan kasuwan, Alhaji Gidado Hassan, wanda ke shugabantar kasuwar raguna a Jalingo farmaki a gidansa dake ƙauyen Audi, misalin ƙarfe 2:00 na dare.

Masu garkuwa da mutane sun halaka dan kasuwa, sun sace matarsa da yaransa
Masu garkuwa da mutane sun halaka dan kasuwa, sun sace matarsa da yaransa Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Daily Trust ta gano yadda ƴan bindigan da za su kai sha-biyu suka kutsa cikin gidan ɗan kasuwan.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kutsa har cikin gida, sun bindige Shahararren ɗan kasuwa har Lahira

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An sake tattaro yadda makasan suka tasa keyar ɗan kasuwan da iyalinsa zuwa wani wuri da ba'a sani ba, inda suka harbe shi gami da barin gawarsa.

Haka zalika, an birne marigayi Gidado Hasaan a babbar maƙabartar Jika Da Dari misalin karfe 9:30 na safiyar Alhamis.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi ne ya tabbatar da aukuwar lamarin.

'Yan bindiga sun kai sabon hari Zamfara, sun sheke dagacin kauye da wasu mutum 19

A wani labari na daban, a kalla mutane goma sha tara ne ‘yan bindiga suka kashe a kauyen Ganar-Kiyawa da ke gundumar Adabka a karamar hukumar Bukkuyum a jihar Zamfara.

Harin na kwanan nan dai ya faru ne da safiyar Lahadi da misalin karfe 8:30 na safe, inda ‘yan bindigar suka afkawa al’ummar garin inda suka fara harbe-harbe babu dadewa, inda suka kashe mutane 20 ciki har da dagacin kauyen.

Kara karanta wannan

Daga karshe, Ministan Buhari ya yi faɗi shirinsa kan takarar shugaban ƙasa a 2023

Tashar Talabijin ta Channels ta ruwaito cewa ‘yan bindigar sun sake kai hari a wasu kauyukan da ke kewaye, inda suka balle shaguna tare da kwashe wasu kayayyaki masu daraja

Asali: Legit.ng

Online view pixel