'Yan bindiga sun kai sabon hari Zamfara, sun sheke dagacin kauye da wasu mutum 19

'Yan bindiga sun kai sabon hari Zamfara, sun sheke dagacin kauye da wasu mutum 19

  • A kalla mutane 19 da suka hada da mata da yara ne suka rasa rayukansu sakamakon farmakin miyagu a kauyen Ganar-Kiyawa
  • Mummunan harin ya auku ne a ranar Lahadi da ta gabata wurin karfe 8:30 na safe inda miyagun suka halaka har da dagacin kauyen
  • Mazauna yankin sun tabbatar da cewa miyagun sun dinga harbe-harbe kafin su fasa shaguna tare da kwashe kadarorin jamaa

Zamfara - A kalla mutane goma sha tara ne ‘yan bindiga suka kashe a kauyen Ganar-Kiyawa da ke gundumar Adabka a karamar hukumar Bukkuyum a jihar Zamfara.

Harin na kwanan nan dai ya faru ne da safiyar Lahadi da misalin karfe 8:30 na safe, inda ‘yan bindigar suka afkawa al’ummar garin inda suka fara harbe-harbe babu dadewa, inda suka kashe mutane 20 ciki har da dagacin kauyen.

Kara karanta wannan

Shugabar APC ta mutu a wajen musayar wuta tsakanin ‘Yan bindiga da ‘Yan banga

'Yan bindiga sun kai sabon hari Zamfara, sun sheke dagacin kauye da wasu mutum 19
'Yan bindiga sun kai sabon hari Zamfara, sun sheke dagacin kauye da wasu mutum 19. Hoto daga channelstv.com
Asali: UGC

Tashar Talabijin ta Channels ta ruwaito cewa ‘yan bindigar sun sake kai hari a wasu kauyukan da ke kewaye, inda suka balle shaguna tare da kwashe wasu kayayyaki masu daraja

Wata majiya daga yankin da ta nemi a sakaya sunanta ta ce al’ummomin da ke karkashin gundumar Adabka sun sha fama da hare-hare da sace-sace daga ‘yan fashin.

“Harin na ranar Lahadi babba ne; kusan kullum suna zuwa su yi awon gaba da mutane, manyan mata, da yara,” majiyar ta shaida wa gidan talabijin na Channels.

Ya ce jamaar Ganar Kiyawa su kan kwana a cikin daji saboda tsoron kada miyagun ‘yan bindiga su kai musu hari a gidajensu.

Da aka tambaye shi game da martanin da hukumomin tsaro suka yi yayin farmakin, ya ce sojoji sun tsaya ne kawai a Adabka da garin Gwashi, lamarin da ya sa wasu kauyukan suka fuskanci hare-haren ‘yan bindiga.

Kara karanta wannan

Zamfara: Mun dauki masu gadin al’umma 4200 don yaki da ‘yan ta'adda

“Hukumomin tsaro ba su isa su kai duk kauyukan da ke kewaye ba. Muna da sojoji a manyan wurare guda biyu, garin Adabka, da Gwashi. Duk sauran kauyukan da ke kusa da su jami’an tsaro ba su gano su ba don haka ’yan bindiga za su iya fita a duk lokacin da suka ga dama su far wa mutane,” yace.

Hukumomin 'yan sanda a jihar har yanzu ba su tabbatar da sabon harin ba.

'Yan ta'adda sun sace mutum 75 a samamen da suka kai kauyukan Zamfara

A wani labari na daban, 'yan ta'adda da ake zargin 'yan bindiga ne sun sace a kalla mutum 75 a yankin Kekun Waje ta karamar hukumar Bungudu a jihar Zamfara.

A wani samame da miyagun suka kai sama da wata daya da ya gabata, sun yi garkuwa da sama da mutum 60.

Wadanda aka sace a wancan lokacin har yanzu suna hannun miyagun, Daily Trust ta ruwaito hakan. Mazauna yankin sun sanar da cewa miyagun na cigaba da kai farmaki daban-daban yankin bayan 'yan sa kai sun sanya musu ido.

Kara karanta wannan

Ta hadu da bacin rana: An kama wata gurguwar karya tana bara, an tursasa ta yin tafiya a bidiyo

Asali: Legit.ng

Online view pixel