Ta'addanci: Yan bindiga sun kashe babban Basaraken gargajiya a Filato

Ta'addanci: Yan bindiga sun kashe babban Basaraken gargajiya a Filato

  • Yan bindiga sun halaka Basaraken gargajiya a jihar Filato, yayin da yake kan hanyar zuwa gaida mara lafiya a Asibiti
  • Wani mazaunin yankin ya ce tuni aka ɗakko gawarsa aka mata jana'iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada
  • Maharan waɗan da ake zaton yan fashi da makami ne, sun farmaki Sarakuna biyu, ɗayan ya koma gida, sun tafi da Motar

Plateau -Wasu yan bindiga da ake tsammanin yan fashi da makamai ne sun farmaki Sarakunan gargajiya biyu a ƙauyen Yala, karamar hukumar Wase a jihar Filato.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa maharan sun kashe ɗaya daga cikin su mai suna, Mustafa Ibrahim, wanda ke rike da sarautar Garkuwan Yala.

Yan bindiga sun kashe basarake a Filato.
Ta'addanci: Yan bindiga sun kashe babban Basaraken gargajiya a Filato Hoto: punchng.com
Asali: Twitter

Lamarin ya faru ne kwana ɗaya tal bayan wasu yan bindiga sun kai hari ƙauyen Pinau a wannan yankin, inda suka yi gaba da ɗaruruwan dabbobi kuma suka kona gidaje da kayan abinci.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun sako mutum 75 a Zamfara, sun faɗi yadda suka yi da mace ɗaya

Wani mazaunin yankin ƙaramar hukumar Wase, Abdullahi Adamu, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, inda ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Sarakunan suna cikin mota a kan hanyarsu ta zuwa Asibiti dake kusa da garin Wase domin gaida mara lafiya lokacin da yan ta'addan suka farmake su."
"Tuni jami'an yan sanda suka ɗakko gawar Marigayi Mustapha Ibrahim suka miƙa wa iyalansa. Mun je wurin da lamarin ya faru da safiyar yau Alhamis."
"An gudanar da Jana'izar Mamacin kamar yadda Addini ya koyar. Ɗayan da suke tare kuma, Magajin garin Yola, Muhammadu Adamu, ya koma gida lafiya, amma maharan sun tafi da motar."

Yayin da aka tuntuɓi kakakin rundunar yan sanda na jihar Filato, ASP Ubah Gabriel, ya yi alkawarin zai nemi manema labarai daga baya kan cigaban amma har yanzun shiru.

A wani labarin kuma Yadda aka gano wata budurwa da aka yi garkuwa da ita tsawon shekara uku ɗauke da ciki wata 8

Kara karanta wannan

Yadda wani ɗan kasuwa ya halaka yan bindigan da suka yi garkuwa da shi, ya koma gida lafiya

Yan sanda sun ceto wata dalibar Sakandire mai shirin rubuta WAEC da ta ɓata shekara uku kenan ɗauke da juna biyu.

An kama matashi da mahaifiyarsa da suka haɗa baki suka sace ta, budurwar tace sun bata wasu kwayoyi ya sa ta manta gida.

Asali: Legit.ng

Online view pixel