Jinkiri alheri: Duk da shafe shekaru biyu a aji daya a jami'arsu, yanzu ta gama da '1st Class'

Jinkiri alheri: Duk da shafe shekaru biyu a aji daya a jami'arsu, yanzu ta gama da '1st Class'

  • Wata ‘yar Najeriya mai suna Ogunsanya Oluwafunke Esther, ta kammala karatunta na digiri da sakamako mai kyau duk da kuwa ta samu tsaiko a makaranta
  • Shekarunta na farko da na karshe a jami'a sun kasance masu kunci, ta yi shekaru hudu maimakon biyu, lamarin da bai kamata ba a tsarin jami'a
  • 'Yan Najeriya da dama sun taya ta murna yayin da wasu daliban da ke kammala karatunsu na digiri suka ce suna fuskantar irin wannan jinkiri a yanzu

Wata ‘yar Najeriya mai suna Ogunsanya Oluwafunke Esther, ta bayyana a yanar gizo domin nuna farin cikinta kan kammala digirin farko da sakamako mafi kyau (1st class).

A wani rubutu da ta yi a Twitter, budurwar ta bayyana cewa ta bata shekaru biyu (2016 da 2017) a ajin farko na jami'a. Hakan ya sake faruwa da ita a shekararta ta karshe yayin da ta sake shafe shekaru biyu (2020 da 2021) a ajin na karshe.

Kyakkyawa ta gama da jami'a da 1st Class
Jinkiri alheri: Duk da shafe shekaru biyu a aji daya a jami'arsu, yanzu ta gama da '1st Class' | Hoto: @thefunkeoguns
Asali: Twitter

Wani jinkirin alheri ne

Oluwafunke ta bayyana cewa jinkiri ba komai bane wani lokacin face alheri, domin a karshe ta cimma burinta. Budurwar dai ta godewa Allah bisa wannan nasara da ta samu.

Budurwar ta kuma yada hotunanta guda biyu a cikin rigarta ta kammala digiri. ’Yan Najeriya sun shiga sashen sharhin rubutunta, inda suka taya murna tare da bayyana ra'ayoyinsu.

Ya zuwa lokacin rubuta wannan rahoto, rubutun budurwar ya samu dankwale sama da 16,000 tare da daruruwan sharhi. A kasa mun kawo kadan daga sharhin 'yan Twitter:

@APRIL092012 ya ce:

"Matakin farko? Wow. Na taya ki murna 'yar uwa. Dakata, yaya dai mutanen da suke gama karatu da matakin farko yawancinsu mata ne, ina mazan suke?"

@ChiemekaAustin ya ce:

"Na taya ki murna. Amma wacce jami'a don Allah. Saboda shekaru 4 yanzu kuma har yanzu a shekara ta 3 nake kuma fannin injiniyanci ne."

@Itz_Oluwatoba:

"Daliban matakin farko galibi mata ne kyawawa sosai... Wannan yasa littafi ke saurin shiga jikinsu."

Haziki: Yadda makaho dan Najeriya ya kirkiri wayoyin salula, bai taba shiga jami'a ba

A wani labarin, John Msughter na daya daga cikin dimbin matasan Najeriya da ke baje kolin irin hazakarsu da ke da yawa a kasar.

Mutumin mai shekaru 44, duk da cewa yana da nakasa, ya kera tare da habaka wata wayar salula da ya kira Chelsea Mobile Mate 40 Pro kuma abin daukar hankali, bai yi karau a jami'a ba.

Da yake nuna wayoyin John a Facebook, wani dan jarida da ya bayyana a matsayin abokinsa mai suna Ukah Kurugh ya bayyana cewa John dan asalin jihar Benue yana neman hadin gwiwa domin samar da wayoyin da yawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel