Haziki: Yadda makaho dan Najeriya ya kirkiri wayoyin salula, bai taba shiga jami'a ba

Haziki: Yadda makaho dan Najeriya ya kirkiri wayoyin salula, bai taba shiga jami'a ba

  • Wani dan Najeriya mai fama da matsalar gani mai suna John Msughter ya kera tare da kirkirar wata wayar salula mai suna Chelsea Mobile Mate 40 Pr
  • Chelsea Mobile Mate ba itace wayar farko da John ya kirkira ba kamar yace ya a baya ya kirkira wata a 2018
  • Makahon mai hazaka mai shekaru 44 wanda bai taba karatu a jami'a ba ya riga ya nemi hakkin mallakar kirkirarsa kuma yana neman hadin gwiwar masu zuba jari

John Msughter na daya daga cikin dimbin matasan Najeriya da ke baje kolin irin hazakarsu da ke da yawa a kasar.

Mutumin mai shekaru 44, duk da cewa yana da nakasa, ya kera tare da habaka wata wayar salula da ya kira Chelsea Mobile Mate 40 Pro kuma abin daukar hankali, bai yi karau a jami'a ba.

Kara karanta wannan

Kuɗi ƙare magana: Bidiyon kek ɗin biki yana saukowa daga hadari yasa ƴan biki kurma ihu

Makaho ya kirkiri wayar hannu
Haziki: Yadda makaho dan Najeriyan ya kirkiri wayoyin salula, bai aba shiga jami'a ba | Hoto: Ukah Kurugh
Asali: Facebook

John yana neman hadin gwiwa don samar da wayoyin da ya kera

Da yake nuna wayoyin John a Facebook, wani dan jarida da ya bayyana a matsayin abokinsa mai suna Ukah Kurugh ya bayyana cewa John dan asalin jihar Benue yana neman hadin gwiwa domin samar da wayoyin da yawa.

Ukah ya bayyana cewa hadin gwiwar da ake nema zai kasance ta hanyoyi biyu.

Na farko ga masu tunanin kasuwanci don kera wayoyin da yawa, na biyu kwa ga kwararrun da za su shiga aikin don habaka wayoyin su yi fice a kasuwa.

Dan jaridar ya bayyana cewa, tuni an riga an sayar da bakwai daga cikin wayoyin da John ya kera a kasuwar yanar gizo ta Jumia kuma wasu da dama na nema.

Kara karanta wannan

Shugabancin APC na kasa: Mika kujera wata shiyya ba ka'ida bane, Abdülaziz Yari

Da jarin N250m, Ukah ya ce John da abokan harkallarsa za su iya kera wayoyi 5,000 daga fasahar John mai ban sha'awa.

Ba Chelsea Mobile Mate kadai John ya kirkirar ba

Abin ban sha'awa a labarinsa shine, Chelsea Mobile Mate 40 Pro da aka tallata shafukan sada zumunta ba ita ce wayar farko da John ya kera ba.

A wata tattaunawa ta wayar tarho da wakilin Legit.ng, Victor Duru, John wanda ya fito daga karamar hukumar Kwande a jihar Benue, ya ce a 2019 ne ya kirkiri wayarsa ta farko mai suna Chelsea Mobile K7.

Ya bayyana cewa, Chelsea Mobile wanda aka kera a watan Disamban 2021 itace wayarsa ta biyu.

Chelsea Mobile waya ce mai daukar layukan SIM guda biyu. Sauran fasalolin wayar da ya bayyana ma Legit.ng sun hada da girman RAM da ya kai 2GB, ma'ajiyar bayanai 16GB, da karfin batir har 3000 mAh.

Kara karanta wannan

Jibgegiyar Matata Tana Lakaɗa Min Duka Kuma Bata Nadama, Miji Ɗan Shekara 60 Ya Roƙi Kotu Ta Kashe Aurensa

Ya kuma yiwa fasaharsa garkuwa, kana yi wa kamfaninsa na Chelsea rajista da Hukumar Harkokin Kasuwanci wato CAC.

Ta yaya John ya samu damar kera waya duk da larurar gani?

Game da yadda ya samu damar kera Chelsea Mobile Mate da sauransu duk da kasancewarsa makaho, John ya bayyana cewa abu ne da ya shafi tunani domin ya dade yana son yin wani babban abu da samar da mafita ga matsaloli.

John ya shaidawa Legit.ng cewa ya samu kwarin guiwa ne daga Nnamdi Ezeigbo wanda yana daya daga cikin jiga-jigan da suka samar da fasahar zamani ta kamfanin Tecno.

Injiniyan na manhajar na'ura ya bayyana cewa iyalansa suna da tushe sosai da kaunar fannin sadarwa da kere-kere na ICT.

John wanda ya mallaki takardar shedar kasa da kasa guda biyu akan yarukan kwamfuta musamman yaren java a MIT ta Lagos kafin ya makance ya ce yana da zanen yadda wayar zata kasance sai kawai ya kaita wata masana’anta.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: 'Yan Najeriya ke son na tsaya takara, ba wai son raina bane, inji Atiku

A cewarsa:

"Komai yana fitowa ne daga tunani. Ina da zane-zanen wayar sai na kai shi wata masana'anta ta kasar China inda aka kera ta bisa ga bayanan da na bayar."

Ya yi nuni da shirinsa na samar da waya ta uku ga makafi. John ya rasa ganinsa ne a 2018 lokacin da ya kamu da cutar glaucoma kuma yana tafiyar da wata kungiyar magance irin wannan cutar - John Lan Eye Foundation.

Martanin 'yan soshiyal midiya

Jude Ahom ya ce:

"Abin ban sha'awa sosai zan so in san cikakkun bayanai na wannan wayar. Ba na son kulob din kwallon kafa na Chelsea amma Chelsea sunan wani ne don haka ba wani babban abu bane. Ina shirin samun sabuwar waya, wannan dai ita ce ta gaba."

Director Goodluck ya ce:

"Na taya ka murna! Na taya ka murna!!
“Yayin da wasu matasa ‘yan da ke da dama ke can suna ikirarin babu wani aikin dogaro da kai a gare su.

Kara karanta wannan

Haba N1k: Yiwa direban NAPEP kyautar N1k bayan dawo da wayoyi 10 da ya tsinta ya bar baya da kura

"Allah ya yiwa wannan mutumin albarka ."

Teseer Jekyll ya ce:

"Ya yi kyau. Ko da yake har yanzu ina mamakin aikin wayar salulan. Tsarinta yana da karfi ko dai ya yake."

Dan shekara 21 nake son aure: Yar shekara 70 da bata taba aure ba, bata taba sanin namiji ba

A wani labarin, wata mata yar shekara 70 mai suna Genevieve wacce bata taba aure ba ko saurayi ko sanin namjiji ba ta bayyana irin namijin da take so.

Genevieve na fama da nakasar kafa wanda ke hanata tafiya.

A hirar da tayi da Afrimax, matar ta bayyana cewa ba haka aka haifeta ba a shekarar 1952. Amma daga baya iyayenta suka gani bata iya tafiya sai da rarrafe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel