An gano wata budurwa da aka yi garkuwa da ita tsawon shekara uku ɗauke da ciki wata 8

An gano wata budurwa da aka yi garkuwa da ita tsawon shekara uku ɗauke da ciki wata 8

  • Yan sanda sun ceto wata dalibar Sakandire mai shirin rubuta WAEC da ta ɓata shekara uku kenan ɗauke da juna biyu
  • An kama matashi da mahaifiyarsa da suka haɗa baki suka sace ta, budurwar tace sun bata wasu kwayoyi ya sa ta manta gida
  • Bayanan yan sanda ya nuna cewa mutanen biyu da ake zargin sun amsa laifukansu, kuma za'a maka su Kotu

Ekiti - Tsawon shekara uku, wata budurwa ta bar gida domin halartar darasi na musamman a shirin da take na zana jarabwar WAEC, iyayenta suka neme ta suka rasa a watan Maris, 2019.

Jami'an yan sanda a jihar Ekiti sun kama wata mata Felicia Ademiloye, da ɗanta, Adewumi, bisa zargin hannu a garkuwa da yarinyar, amfani da ita da kuma fyaɗe.

Kara karanta wannan

Shugabancin APC: Jerin Sunayen yan takarar da suka yi fatali da umarnin Buhari, suka mika Fam Hedkwata

Mahaifiyar budurwar da ta ɓata, a ranar 15 ga watan Maris, ta samu labarin inda ɗiyarta take, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Adewumi da mahaifiyarsa
An gano wata budurwa da aka yi garkuwa da ita tsawon shekara uku ɗauke da ciki wata 8 Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Bayan samun bayanai, Dakarun yan sanda suka bibiyi yarinyar har zuwa gidan Ademiloye kuma suka ceto ta sannan suka kama matar da ɗanta.

Kakakin yan sanda na jihar Ekiti, ASP Sunday Abutu, a wata sanarwa, yace bincikensu ya nuna cewa matashin ne ya sace yarinyar a ranar da ta ɓata, ya kaita gidan mahaifiyarsa.

Punch ta rahoto Abutu ya ce:

"Yarinyar da lamarin ya faru da ita tace bayan ta sha kwayoyin da Adewumi ya kawo mata, bata ƙara tunanin komawa gida ba. Tace yanzu ta zama yar kwaya saboda sabo na tsawon shekara uku."
'Adewumi ya sadu da ita lokuta da dama kuma ya kawo maza kala daban-daban sun kwanta da ita a duk lokacin da yaji aljihunsa ba kuɗi, suna ba shi dubu N10,000 zuwa N20,000."

Kara karanta wannan

Wani bawan Allah ya lakaɗa wa Matarsa dukan kawo wuka har Lahira kan karamin abu

Kakakin yan sandan ya ƙara da cewa binciken Likitoci ya nuna cewa budurwan na ɗauke da juna biyu na watanni Takwas.

Shin waɗan da ake zargi sun amsa laifin su?

Wanda ake zargi a yayin binciken yan sanda, Adewumi ya amsa laifinsa kuma bisa haka da shi da mahaifiyarsa za su gurfana a gaban Kotu bisa tuhumar haɗa baki da yin garkuwa, fyaɗe da amfani.

A wani labarin kuma Maraba da Ramadan: Gwamnatin Ganduje ta umarce makarantu su ba ɗalibai hutu

Yayin da Musulmai ke ta shirin tarban babban bako, gwamnatin Kano ta yi wani muhimmin gyara a Kalandar makarantun Firamare.

Gwamnatin karkashin gwamna Ganduje ta ba da umarnin rufe Firamaren gwamnati da masu zaman kansu saboda Ramadan.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel