Dan shekara 21 nake son aure: Yar shekara 70 da bata taba aure ba, bata taba sanin namiji ba

Dan shekara 21 nake son aure: Yar shekara 70 da bata taba aure ba, bata taba sanin namiji ba

  • Wata mata yar shekara 70 mai suna Genevieve ta bayyana cewa tana bukatan saurayi dan shekarar 21
  • Matar wacce ke da nakasar kafa bata taba fita daga gidanta ba kuma bata taba saurayi ba
  • Genevieve ta kwashe wadannan shekaru tana rayuwa cikin gida sakamakon cutar da ta hanata amfani da kafafunta

Wata mata yar shekara 70 mai suna Genevieve wacce bata taba aure ba ko saurayi ko sanin namjiji ba ta bayyana irin namijin da take so.

Genevieve na fama da nakasar kafa wanda ke hanata tafiya.

Bata taba saurayi ko makaranta ba

A hirar da tayi da Afrimax, matar ta bayyana cewa ba haka aka haifeta ba a shekarar 1952. Amma daga baya iyayenta suka gani bata iya tafiya sai da rarrafe.

Ana kyautata zaton cewa Genevieve ta kamu da cutar ne lokacin tana yarinya wanda ya nakasa kafafunta.

Kara karanta wannan

Duk da Kyauna, “Samarin Shaho” Guduna Suke yi, Budurwa Mai Kamun Kai Tayi Bayani

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sakamakon haka iyayenta basu sa ta a makaranta ba saboda basu da kudin keken guragu kuma ba zasu iya rika kaita makaranta kullum ba.

Yar shekara 70
Dan shekara 21 nake son aure: Yar shekara 70 da bata taba aure ba, bata taba sanin namiji ba Hoto: Afrimax
Asali: UGC

Makwabtanta suka kai mata dauki

Bayan rasuwar iyayenta, makwabtanta suka kawo mata dauki suna kai mata abinci jefi-jefi.

Ta bayyanawa dan jaridan dake hira da ita cewa tana bukatan saurayi dan shekara 21 matsayin masoyi kuma tana son aure.

Kalli bidiyon:

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel