Kada Ku Tafi Yajin Aiki, IGP Ya Roƙi Ƴan Sandan Najeriya

Kada Ku Tafi Yajin Aiki, IGP Ya Roƙi Ƴan Sandan Najeriya

  • A ranar Laraba, Sifeta janar na ‘yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba ya roki arziki a wurin ‘yan sandan masu shirin tafiya yajin aiki
  • IGP din, wanda ya samu wakilcin mataimakin sa mai kula da yankin kudu maso yamma, Johnson Kokumo, ya yi wannan rokon a ofishin ‘yan sandan na zone 2
  • Ya bukaci su yi dubi akan yadda mutane suke ba su goyon baya da kuma kokarin da gwamnatin tarayya da shugabanninsu suke yi na gyara musu rayuwa

Sifeta Janar na ‘yan sanda, IGP, Usman Alkali Baba a ranar Laraba ya roki ‘yan sandan kasar nan akan cewa kada su tafi yajin aikin da suke shirin tafiya, Nigerian Tribune ta ruwaito.

IGP din wanda ya samu wakilcin mataimakinsa da ke kulawa da yankin kudu maso yamma, Johnson Kokumo, ya bayyana wannan bukatar ta shi a ofishin rundunar ‘yan sanda na Zone 2 da ke Onikan yayin da ya ke zagaye rundunonin ‘yan sanda da ke yankin kudu maso yammacin Najeriya.

Kara karanta wannan

IGP na ya sanda ya jinjinawa Sajen Yahaya da ya ki amsan cin hancin N300,000

Kada Ku Tafi Yajin Aiki, IGP Ya Roƙi Ƴan Sandan Najeriya
IGP Ya Roƙi Ƴan Sandan Najeriya Kada Su Tafi Yajin Aiki. Hoto: Nigerian Tribune
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban ya roki ‘yan sandan inda ya ce ya kamata su duba yadda jama’a suke ba su hadin kai da kuma yadda shugabannin su da gwamnatin tarayya suke kokarin inganta musu rayuwa a kasar nan.

DIG din ya ce:

“Na zo da sako daga sifeta janar na ‘yan sanda wanda ya shawarce mu akan dagewa da kuma tsayawa akan ayyukan mu.
“Ya kamata mu nuna kwarewa a duk ayyukan da za mu yi sakamakon yadda ko wanne bangare da aikin mu ya ke yana da dokokin da aka shimfida. Bari in tuna muku, haramun ne dan sanda ya tafi yajin aiki, saboda hakan yana da illa mai yawa.”

Ya yanko musu wata aya daga cikin bibul

Ya ci gaba da cewa:

“Ku tuna da taken nan da ya ke cewa, dan sanda abokin kowa, don haka in har ku ka kawo cikas wurin dakile harajin da ake amfani da shi wurin sallamar ku, hakan sai ya taba ku.

Kara karanta wannan

2023: Saraki, Tambuwal da ‘Yan takaran Arewa za su hada kai, domin tsaida mutum 1 a PDP

“Idan mun yi abu mai kyau, jama’a zasu yaba mana. Kuma idan mun yi mara kyau, za su soke mu. Idan za ku tuna, bibul ya ba mu makullin aljana saboda ya nuna cewa duk mai samar da zaman lafiya zai shiga aljanna.”

Nigerian Tribune rahoto cewa shugaban yace su masu kawo zaman lafiya ne da kuma kwantar da tarzoma, don haka Ubangiji yana ganin su. Matsawar suka tozarta amanar da aka ba su ta kulawa da mutane, za a samu matsala. Don yajin aiki yana da illa mai yawa.

Ya kara da kwantar musu da hankali inda ya ce yanzu haka ana duba akan yadda za a gyara albashin su don ba kara-zube ake yin hakan ba.

Ya ce yanzu haka an samar da kayan aikin da zasu saukaka musu ayyuka

Ya ce sai ministoci sun duba kuma shugaban kasa ya bayar da umarni sannan za a kaddamar. Sannan gwamnati ta rangwanta musu akan haraji, don haka ba a cire haraji a albashinsu.

Kara karanta wannan

Kamfanonin sadarwa su na maganar kara farashin yin wayar salula saboda tsadar mai

Ya ci gaba da bayyana cewa IGP ya bayar da umarnin horarwa ga jami’ai. Kuma ya bukaci a kara daukar wasu ‘yan sandan. Ya ce yanzu haka ana kara gini da gyare-gyaren bariki da ofisoshin ‘yan sanda da ke fadin kasar nan.

Ya tabbatar musu da cewa IGP ya bukaci ‘yan sanda su je hedkwatar su don amsar kayan aiki wadanda za su saukaka musu ayyukan su.

Amma a cewarsa, sai sun yi hakuri kuma sun kwantar da hankulan su sannan za a kai inda ake son zuwa. Ya ci gaba da rokon su inda ya ce kada su kuskura su tafi yajin aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel