IGP na ya sanda ya jinjinawa Sajen Yahaya da ya ki amsan cin hancin N300,000

IGP na ya sanda ya jinjinawa Sajen Yahaya da ya ki amsan cin hancin N300,000

  • Shugaban yan sandan Najeriya ya yabawa wasu jami'ansa da suka kamanta gaskiya a bakin aiki
  • Cikin mutum uku da ya jinjinawa, daya ya ki karban cin hancin N300,000 a kotu dake jihar Zamfara
  • IGP Alkali ya yi alkawarin cewa za'a inganta albashi da alawus na jami'an yan sanda don jin dadinsu

Abuja - Sifeto Janar na yan sanda, IGP Baba Alkali, ya jinjinawa wasu jami'an yan sanda biyu da suka nuna kwarewa wajen aikinsu ta hanyar fin karfin zukatarsu kan kudi.

IGP ya ce ya kamata a rika yabawa yan sanda irin wadannan da suka ki bin son zuciyarsu tare da gyara sunan hukumar.

Shugaban yan sandan ya jinjinawa Sergeant Yahaya Ahmed wanda wani Chukwuka Jude ya baiwa cin hancin naira dubu dari uku amma yaki amsa.

Kara karanta wannan

Zulum ya rabawa leburori 846 kudi N62m: Dattawa sun samu N100,000; matasa sun samu N50,000

Hakazalika wani jami'i Samson Ekikrere wanda ya kwato jakar kudin wani kuma ya mayar masa da shi.

IGP na ya sanda ya jinjinawa Sajen Yahaya
IGP na ya sanda ya jinjinawa Sajen Yahaya da ya ki amsan cin hancin N300,000 Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A jawabin da kakakin hukumar yan sanda ya saki a shafin Tuwita, yace:

"IGP ya jinjinawa SGT Sampson Ekikere, na 22 Police Mobile Force, Ikeja, Lagos, bisa jajircewarsa na ranar 19 ga Maris, 2022 lokacin da ya kwato jakar kudi, na wani Lukman Abaja kuma ya nemesa har ya mika masa."
"Hakazalika Sajen Yahaya Ahmed na kotun Sharia dake Tudun Wada Gusau Zamfara wanda ya ki amsan kudin cin hanci N300,000 hannun wani Chukwuka Jude, wanda aka damke a kotu ranar 18 ga Junairu, 2022 kan laifin zamba."

Sifeto Janar IGP Alkali ya amince Mata yan sanda su fara sanya Hijabi

A wani labarin kuwa, sifeto Janar na yan sanda, IGP Baba Alkali, ya amince jami'an yan sanda mata su fara sanya dan kwali mai kama da Hijabi kan kayan sarki.

Kara karanta wannan

Anambra: Laifuka 3 da suka jawo aka kama tsohon gwamna Obinao garin tserewa Amurka

Wannan ya bayyana a hotunan sanarwar da hukumar tayi kwanakin nan.

An bayyana sabon tsarin ne a ganawar IGP na manyan jami'an yan sanda ranar 3 ga Maris 2022.

IG Baba ya bayyana cewa hukumar yan sanda na da jami'ai a dukkan kananan hukumomin jihar mai mutane masu mabanbantan addini da al'ada.

Saboda haka akwai bukatar girmama addinan mutane don kwantar musu da hankali wajen gudanar da ayyukansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel