2023: Saraki, Tambuwal da ‘Yan takaran Arewa za su hada kai, domin tsaida mutum 1 a PDP

2023: Saraki, Tambuwal da ‘Yan takaran Arewa za su hada kai, domin tsaida mutum 1 a PDP

  • Tsohon shugaban majalisa yana neman yadda PDP za ta fitar da ‘dan takara hankali kwance a 2023
  • Bukola Saraki ya hadu da Gwamnonin Arewa da ke harin kujerar shugaban kasa a karkashin PDP
  • Saraki, Tambuwal da Bala sun yarda su zauna domin a tsaida wanda zai yi wa PDP takara a cikinsu

Bauchi - Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da wasu gwamnonin PDP biyu za su yi kokarin ganin an samu hadin-kai a zaben fitar da 'dan takara.

Daily Trust ta fitar da wani rahoto a ranar Lahadi, 20 ga watan Maris 2022 inda aka ji cewa Bukola Saraki da Aminu Tambuwal sun ziyarci gwamnan Bauchi.

‘Yan siyasar sun tattauna da Sanata Bala Mohammed wanda yana cikin masu neman takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar hamayya ta PDP a 2023.

Bukola Saraki ya zanta da ‘yan jarida bayan taron da suka yi, ya ce sun ga bukatar a zauna, domin tsara abin da ya fi dacewa a game da takarar shugaban kasa.

“A wajen yin wannan, mun hadu mun tattauna a kan 2023 da mu ke hange, zaman lafiya da hadin-kai da cigaban kasar nan ya fi karfin burin daidaikunmu.”
Saraki, Tambuwal a Bauchi
Saraki, Bala da Tambuwal Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Jawabin Bukola Saraki

“Mun yi zama kan muhimmancin mu hada-kai, mu yi aiki tare. Mun yi imani kan dukkanmu ukun nan a hade yake, mun dage domin cin ma manufa.”
“Mun yaba da dukkanmu uku mu ka nuna bukatar mu jagoranci kasar nan, sannan mun fahimci dukkaninmu, mun cancanci mu shugabanci kasar nan.”
“A karshe mutum daya ne zai zama shugaban kasa a 2023; mun kuma yarda za mu yi aiki tare domin a fito da ‘dan takara ta hanyar maslaha.” - Saraki

An rahoto tsohon gwamnan na jihar Kwara yana cewa za su yi kokari wajen ganin an samu kwanciyar hankali a PDP, a cewarsa hakan zai kawo zaman lafiya a kasa.

Za a zauna da Atiku

Punch ta ce su Saraki za su yi zama da Atiku Abubakar domin fada masa matsayar da suka dauka.

Tsohon mataimakin shugaban kasar yana cikin masu neman tsayawa takara a jam’iyyar PDP. Atiku ne ya samu tikitin PDP a 2019, ya doke su Saraki da Tambuwal.

Siyasar Kano sai Kano

Dazu ku ka ji cewa Murtala Garo Nasiru Gawuna, Sanata Barau Jibrin, da tsohon shugaban majalisar dokoki, Hon. Rurum su na cikin masu neman Gwamnan Kano.

A cikin masu harin kujerar Ganduje a zaben 2023, ana tunanin akwai Abba Kabir Yusuf watau Abba Gida Gida yayin da wa’adin Ganduje zai cika a shekara mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel