Kotu ta yankewa barawon Al-kur'ani hukucin sharan masallaci na kwanaki 30 a Kano
- A birnin Kano, an yanke wa wani mutum hukuncin share masallaci na tsawon kwanaki 30 a jere
- An yanke masa hukuncin ne bisa zarginsa da aka yi shiga masallaci tare sace Alkur'ani gida takwas
- Wanda aka hukunta da kansa ya amsa laifinsa bayan da aka gurfanar da shi a gaban wata kotun shari'a
Kano - Wata kotun shari’a da ke zama a Fagge 'Yan-Alluna a Kano ranar Talata 17 ga watan Agusta ta umarci Halifa Abdullahi da ya share masallacin Juma’ar Fagge na tsawon kwanaki 30 a jere a matsayin hukuncinsa na satan kwafin Alkur’ani mai girma guda takwas.
Mista Abdullahi, mazaunin unguwar Yola da ke cikin birnin Kano, an zarge shi da sata a masallaci a unguwar Tudun Maliki ranar Lahadi da daddare tare da kwashe kwafin Alkur'ani guda takwas.
Sai dai jami'an tsaron masallacin sun cafke wanda ake zargin bayan ya aikata laifin, Daily Nigerian ta ruwaito.
An gurganar dashi a gaban kotu
Don haka masu gadin sun mika shi ga ofishin 'yan sanda na Filin Hockey, wanda a ranar Talata ya gurfanar da shi a kotun Shari'a.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Lokacin da mai gabatar da kara na 'yan sanda, Abdul Wada, ya karanto tuhumar da ake yi wa Abdullahi, nan da nan ya amsa laifinsa.
Don haka alkalin kotun, Bello Musa-Khalid, ya yanke masa hukuncin share farfajiyar babban masallacin Juma’ar Fagge, na tsawon kwanaki talatin a jere.
Rahoto na cewa ana kallon masallacin Juma'a na Fagge a matsayin mafi girma a jihar.
Abduljabbar ya rame: Sheikh Abduljabbar ya sake gurfana a gaban kuliya
Rahoto ya bayyana cewa, an sake kai Malam Abduljabbar Nasir Kabara gaban kotu a bisa tuhumarsa da yin kalaman tunzura jama'a da batanci ga Annabi SAW. Zargin da Malamin ya musanta a baya.
Legit Hausa ta tattaro muku, a ranar 30 ga watan Yulin da ta gabata aka fara shari'ar Abduljabbar Nasir Kabara, inda aka gabatar da takardar korafi a kansa.
A cewar gwamnati, an gurfanar da Malamin Abduljabbar, bisa kaurin suna da ya yi wajen yin wa'azin da ke haifar da mahawara da kuma zargin furta kalaman batanci ga Annabin SAW.
A cewar wakilin BBC da ke cikin kotun da ake sauraren karar ya ce an tsaurara tsaro fiye da zaman kotun da aka yi a farko.
Batun Abba Kyari: Kwamiti ya gama bincike, ya mika rahoto ga Sufeto-Janar
A wani labarin, Kwamitin Bincike na Musamman ya mika rahotonsa ga Sufeto Janar na 'yan sanda, Usman Baba, makonni biyu bayan da aka umarce shi da ya binciki tsohon Shugaban rundunar IRT kuma Mataimakin Kwamishinan' Yan sanda, Abba Kyari.
Kwamitin na mutum hudu karkashin jagorancin Mataimakin Sufeto -Janar na 'yan sanda mai kula da sashin binciken manyan laifuka na rundunar, Joseph Egbunike, ya mika sakamakon binciken ga IG ranar Litinin 16 ga watan Agusta.
A baya mun rahoto cewa, hukumar FBI ta kasar Amurka ta zargi Abba Kyari da hannu cikin wata damfara da Abbas Ramon (Hushpuppi) ya yi kan wani dan kasuwar Qatar, Punch ta ruwaito.
Asali: Legit.ng