Tashin hankali yayin da aka sace motar dan jarida a wurin dauko rahoto a sakateriyar APC

Tashin hankali yayin da aka sace motar dan jarida a wurin dauko rahoto a sakateriyar APC

  • Wasu sun sace motar editan kamfanin jarida yayin da ya je daukar rahoto a sakateriyar jam'iyyar APC
  • Rahoton da muka samo ya bayyana cewa, ya gano an sace motar ne bayan da aka kammala taron siyasar
  • Ya zuwa yanzu dai ya shaidawa manema labarai 'yan uwansa cewa, an sanar da jami'an tsaro da sauran wadanda abin ya shafa

An sace wata mota kirar Golf 3 samfurin Amurka mai lamba L S D-516-HB mallakin Editan Siyasa na jaridar New Nigerian Newspaper (NNN), Amos Mathew.

Rahoton jaridar Vanguard ya ce, an aje motar ne mai launin baki a gaban sakatariyar jam’iyyar APC, inda aka gayyaci ‘yan jarida domin daukar rahotannin bayyana dan takarar gwamna na jam’iyyar APC.

An sace motar dan jarida
Tashin hankali yayin da aka sace motar dan jarida a wurin dauko rahoto a sakateriyar APC | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Mista Mathew ya ce ya ajiye motar ne a gaban Sakatariyar da misalin karfe 10:00 na safe, kuma ya gano an sace motar ne a karshen taron da misalin karfe 11:20 na safiyar ranar Talata.

Kara karanta wannan

2023: Mulkin Buhari ba komai bane face yaudara, dan takarar shugaban kasa na PDP

Hakazalika, ya ta'allaka zargin sace motar ga wasu matasa 'yan bangar siyasa da ba gano ko su wanene ba har zuwa yanzu, kamar yadda jaridar Daily Sun ta ruwaito.

A cewarsa:

"An sanar da 'yan sanda da sauran hukumomin da abin ya shafa game da mummunan lamarin..
“Sauran kayayyaki masu daraja a cikin motar sun hada da katin ATM, katin shaida na ofis, katin zabe, katin shaidar dan kasa da dai sauransu."

Shugabancin APC: Dan takara daga Zamfara ya janye kudirinsa awanni kafin tantancewa

A wani labarin, daya daga cikin yan takarar kujerar shugaban jam'iyyar APC ta kasa, Dakta Sani Shinkafi, ya sanar da janyewa daga tseren neman shugabanci, kamar yadda Channels tv ta rahoto.

Shinkafi, tsohon sakataren jam'iyyar AFGA ta kasa, ya sanar da haka ne a wani taron manema labarai ranar Litini, da daddare a Gusau, babban birnin Zamfara.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Yan sanda sun karbe majalisar Cross River bayan tsige yan majalisa 20

Ya yi bayanin cewa ya dauki wannan matakin ne domin biyayya ga tsarin jam'iyyar APC na kai kujerar shugaba yankin arewa ta tsakiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel