Shugabancin APC: Ɗan takara daga Zamfara ya janye kudirinsa awanni kafin tantancewa

Shugabancin APC: Ɗan takara daga Zamfara ya janye kudirinsa awanni kafin tantancewa

  • Tsohon Sakataren jam'iyyar APGA ta ƙasa, Dakta Sani Shinkafi, ya janye daga tseren takarar shugaban APC na ƙasa
  • Jigon siyasan wanda ya koma APC tare da gwamna Matawalle, ya ce ya yi haka ne domin biyayya ga matakin jam'iyya
  • A cewarsa, yana goyon bayan shugabancin riko na Mala Buni, dan haka yana bayan matakin kai muƙamin arewa ta tsakiya

Zamfara - Ɗaya daga cikin yan takarar kujerar shugaban jam'iyyar APC ta ƙasa, Dakta Sani Shinkafi, ya sanar da janyewa daga tseren neman shugabanci, kamar yadda Channels tv ta rahoto.

Shinkafi, tsohon sakataren jam'iyyar AFGA ta ƙasa, ya sanar da haka ne a wani taron manema labarai ranar Litinin, da daddare a Gusau, babban birnin Zamfara.

Sani Shinkafi
Shugabancin APC: Ɗan takara daga Zamfara ya janye kudirinsa awanni kafin tantancewa Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Ya yi bayanin cewa ya ɗauki wannan matakin ne domin biyayya ga tsarin jam'iyyar APC na kai kujerar shugaba yankin arewa ta tsakiya.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta gamu da babbar matsala, wani jigo tare da dandazon masoya sun koma PDP

Tun da jihar Zamfara ba ta ɗaya daga cikin jihohin yankin, Shinkafi ya yi amannar cewa babu bukatar ya cigaba da fafutukar neman kujerar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A jawabinsa ya ce:

"Na rike muƙamin sakataren jam'iyyar APGA na tsawon shekaru, dan haka nasan matakai da tsarin jam'iyyar siyasa. Zan yi biyayya ga tsarin jam'iyya na kai kujerar arewa ta tsakiya."
"Na san shugabancin jam'iyya, na kuma san muhimmancin girmama na gaba, tun da jam'iyya ta yanke hukunci, bani da wani zaɓi da ya zarce yin biyayya."

Ko meyasa ya janye kudirin?

Tsohon jigon APGA, wanda ya koma jam'iyyar APC tare da gwamna Bello Matawalle na Zamfara a watan Yuni, 2021, ya jaddada cewa ya ɗauki matakin ne da kyakkyawar zuciya.

"Ni a karan kaina ina tare da shugaban kwamitin rikon kwarya na APC ta ƙasa, Mai Mala Buni, ina goyon bayansa kuma ina tare da shi."

Kara karanta wannan

2023: Mulkin Buhari ba komai bane face yaudara, dan takarar shugaban kasa na PDP

A wani labarin kuma Shugabancin APC: Jerin Sunayen yan takarar da suka yi fatali da umarnin Buhari, suka mika Fam Hedkwata

Yayin da ranar 26 ga watan Maris da APC zaɓa don gudanar da babban taronta ke ƙara natsowa, yan takara na cigaba da cike sharudda.

Duk da wasu bayanai sun nuna shugaba Buhari ya nuna zabinsa, amma har yanzun wasu yan takara ba su hakura ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel