Innalillahi: Hadarin mota ya lakume mutane 11 a hanyar Zaria zuwa Kaduna

Innalillahi: Hadarin mota ya lakume mutane 11 a hanyar Zaria zuwa Kaduna

  • Wani mummunan hadarin mota ya hallaka mutane sama da 10 a wani yankin jihar Kaduna ranar Asabar
  • Hadarin ya faru ne sakamakon gudun da direban ke yi da ya wuce misali, kana ya dauki mutane fiye da kima
  • Hukumar kiyaye haddura ta kasa ta yi bayanin yadda lamarin ya faru, ta kuma yi gargadi ga direbobi

Zaria, Kaduna - Mutane 11 ne suka mutu a wani hatsarin mota da ya auku a hanyar Zaria zuwa Kaduna da yammacin ranar Asabar.

An tattaro cewa hatsarin ya afku ne a lokacin da wata mota kirar Toyota Carina mai lamba KTL 251QG, ta kwace a kusa da Nuhu Bamalli Polytechnic da ke Zaria, Daily Trust ta ruwaito.

Kwamandan hukumar kiyaye hadurra na kasa da ke Zaria, Abubakar Tatah Murabus, wanda ya tabbatar da faruwar hatsarin ya ce an kwashe dukkan wadanda abin ya shafa zuwa dakin ajiyar gawa.

Kara karanta wannan

Ramadan: Yadda Jarumin Kannywood, Naburaska Ya Tallafa Wurin Sakin Ƴan Gidan Yari 33

Harain mota ya hallaka mutane
Innalillahi: Hadarin mota ya lakume mutane 11 a hanyar Zaria zuwa Kaduna | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Ya kuma dora alhakin faruwar hatsarin a kan tsala gudu fiye da kima da kuma tukin wuce gona da iri.

Ya ce motar mai kujeru biyar da ta taso daga Kaduna zuwa Bakori a jihar Katsina, cike take da mutane 11.

A cewarsa:

“Hatsarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar da misalin karfe 2 na rana daura da Tariyar Sarki kusa da Nuhu Bamalli Polytechnic, Zaria.
“Don haka ne muke gargadin direbobi da su daina dabi’ar lodin fasinjojin da ke wuce kima.
"Ku yi tunani, wannan motar da aka yi ta don daukar mutane biyar ciki har da direban ta dauki mutane goma sha daya, kuma an ce direban yana gudun wuce gona da iri duk da yawan mutanen da ke cikin motar."

Ya bayyana sunan direban da Musa Iliyasu.

Kara karanta wannan

Kaduna: Baya ga hari a masallaci, 'yan bindiga sun hallaka mutane, sun sace wasu mata

Innalillahi: Mota dauke da silindar gas ta fadi a Kano, ta lalata kayayyaki, ta yi kisa

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da mutuwar mutum daya a wata fashewar da aka samu ta iskar gas da ta afku a kauyen Ijarawa da ke karamar hukumar Bichi a jihar.

Rahoton da jaridar Punch ya bayyana cewa, wani mutum daya ya tsira daga lamarin.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara, Alhaji Saminu Abdullahi ya fitar ranar Litinin a Kano, inda ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da safiyar yau 8 ga watan Fabrairu.

Sanarwar ta ci gaba da cewa:

“Mun samu kiran gaggawa daga Insifeto Daiyabu Tukur da misalin karfe 07:46 na safe cewa wata mota da ke dauke da silindar gas din girki ta fadi a kan titi kuma daya daga cikin kayan ya fashe.

Kara karanta wannan

Yankin Yarbawa zai balle daga Najeriya ba tare da bindiga ba, Sunday Igboho

"Bayan samun labarin, mun aika da tawagarmu cikin gaggawa zuwa wurin da abin ya faru da misalin karfe 8:00 na safe domin ceto wadanda abin ya rutsa dasu."

Hadarin mota: Kwanaki bayan kammala digiri a ABU, matashi da mahaifiyarsa sun rasu a hadari

A bangare guda, labari da muke samu ya nuna cewa Allah ya yiwa wani dalibin jami'ar Ahmadu Bella University (ABU), Zaria, wanda ya kammala karatu kwanan nan, Bashir Maiwada Zubairu, rasuwa.

A wani wallafa da shafin Instablog9ja ya yi a Instagram, an tattaro cewa Maiwada ya rasu ne tare da mahaifiyarsa a wani hatsarin mota.

Mummunan al'amarin ya afku ne a ranar Asabar, 5 ga watan Fabrairu, a hanyar Kano zuwa Katsina.

Asali: Legit.ng

Online view pixel