Hotuna: Shugaba Buhari ya dawo daga Landan bayan shafe kwanaki ana duba lafiyarsa

Hotuna: Shugaba Buhari ya dawo daga Landan bayan shafe kwanaki ana duba lafiyarsa

  • Bayan shafe akalla kwanaki 12 a kasar Burtaniya, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo Najeriya
  • Shugaban ya tafi birnin Landan kusan makwanni biyu da suka gabata domin ganawa da masu duba lafiyarsa
  • Shugaban ya dawo gida a yau Juma'a, inda ya samu tarbar wasu jiga-jigan gwamnati a fadarsa da ke Abuja

Abuja - Yanzun nan muke samun labarin cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dura babban birnin tarayya Abuja, bayan shafe kwanaki da yawa a kasar Burtaniya.

Rahotanni daga fadar shugaban kasa sun bayyana cewa, shugaban ya tafi Landan kwanakin baya domin a duba lafiyarsa.

Daily Trust ta ce ta samo daga NAN cewa jirgin shugaban kasan ya sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja ne da misalin karfe 7.09 na dare.

Kara karanta wannan

Matashi ya biya N20m nakadan don takara a zaben shugaban jam'iyyar APC

Buhari ya dawo daga Landon
Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya dawo daga Landan bayan shafe kwanaki ana duba lafiyarsa | Hoto: Vanguard News
Asali: Facebook

Hadimin Buhari a fannin yada labarai, Bashir Ahmad ya yada hotonn lokacin da shugaban ya sauka daga jirgi jim kadan bayan isowarsa.

Kalli hotunan:

Hakazalika, jaridar Vanguard ta yada karin hotunan dawowar shugaba Buhari daga birnin na Landan.

Kalli karin hotunan:

Wadanda suka tarbi Buhari

Bayan isowarsa ya samu tarba daga shugaban ma’aikatan fadar gwamnati, Farfesa Ibrahim Gambari, ministan babban birnin tarayya (FCT), Malam Muhammed Musa Bello da ministan albarkatun ruwa, Engr. Suleiman Adamu.

Hakazalika da DIG na ‘yan sanda Hassan Sanusi, Darakta Janar na Hukumar Tsaro ta farin kaya (DSS), Mista Yusuf Magaji Bichi, da mai ba da shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina.

Shugaba Buhari zai tafi birnin Landan ganin Likita na tsawon makonni 2

Kara karanta wannan

Rashin wutar lantarki ce matsala mafi girma ga cigabar kasar nan, Tinubu

A tun farko kafin tafiyarsa mun kawo rahoton cewa, shugaba Muhammadu Buhari zai tafi Landan, kasar Birtaniya, don ganin Likitocinsa na tsawon makonni biyu bayan halartan taron majalisar dinkin duniya da za'ayi a Kenya.

Mai magana da yawun Shugaban kasa, Femi Adesina, ya tabbatar da hakan a jawabin da ya saki ranar Talata.

Ya ce:

"Shugaba Buhari zai tashi daga Abuja yau Talata 1 ga Maris don halartan murnar cika shirin majalisar dinkin duniya na yanayi shekaru 50 (UNEP@50), da aka shirya yi ranar 3-4 ga Maris, 2022, a Nairobi, Kenya, sakamakon gayyatar da takwararsa na Kenya, Uhuru Knyatta yayi masa."

Asali: Legit.ng

Online view pixel