Matashi ya biya N20m nakadan don takara a zaben shugaban jam'iyyar APC

Matashi ya biya N20m nakadan don takara a zaben shugaban jam'iyyar APC

  • Matasa sun zabura sun gabatar da nasu dan takaran a zaben shugabannin jam'iyyar APC
  • Said Etsu ya cire kudi, naira na gugan naira milyan ashirin don sayan fam na takara a zaben APC
  • Kwamred Mohammed Saidu Etsu zai yi takara tare da tsaffn gwamnoni, Sanatoci da manyan yan kasuwa

Matashi dan jam'iyyar All Progressives Congress APC, Kwamred Mohammed Saidu Etsu, daga jihar Neja, ya shiga jerin yan takara kujerar shugaban jam'iyyar da za'ayi ranar 26 ga Maris, 2022.

Said Etsu ya garzaya hedkwatar jam'iyyar tare da abokansa don yankar Fam din takara a zaben.

Ya biya kudin Fam naira milyan ashirin kudi a hannu.

Abokinsa, Musa Alhaji Sule, ya bayyana a shafinsa na Tuwita cewa:

"Abokinmu @saiduEtsu, dan takarar kujeran shugaban jam'iyyarmu ta @OfficialAPCNg ya biya kudin milyan 20 kudi a hannu don sayen Fam."

Kara karanta wannan

Sambo, Lawan, Gbajabiamila da wasu jiga-jigai sun dira Ilorin bikin diyar tsohon minista

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hakazalika hadimin gwamnan jihar Neja, AbdulBaqi Ebbo, ya saki hotunansu yayinda Estu ya karbi Fam dinsa.

Kwamred Mohammed Saidu Etsu zai yi takara tare da tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Sanata Abdullahi Adamu; tsohoon gwamnan Zamfara, Alhaji AbdulAziz Yari; tsohon gwamnan Borno, Ali Modu Sherrif; tsohon gwamnan Benue, George Akume; da tsohon gwamnan Nasarawa, Tanko AlMakura.

Sauran sune Salihu Lukman da Sanata Muhammad Sani Musa.

Rikici gabanin taron gangamin APC: Kujerar shugabancin jam'iyya ta raba kan Sanatoci

Batun wanda zai zama shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa ya raba kan masu ruwa da tsaki na jam'iyyar a majalisa.

Sanatoci uku, Tanko Al-Makura daga Nasarawa, Sani Musa daga Neja da Abdullahi Adamu daga Nasarawa ne suke takarar kujerar.

Za a gudanar da babban taron jam'iyyar a ranar 26 ga watan Maris a Abuja, inda za a zabi shugaban jam'iyyar da sauran mambobin kwamitin uwar jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Dankwambo, Fayose, Wike da Aduda na kokarin jan ra'ayin Goje ya koma PDP

Daily Trust ta rahoto cewa wani bincike da ta yi ya nuna cewa wasu sanatoci na goyon bayan Abdullahi Adamu saboda ikirarin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari na goyon bayansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel