Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari zai tafi birnin Landan ganin Likita na tsawon makonni 2

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari zai tafi birnin Landan ganin Likita na tsawon makonni 2

  • Kamar yadda ya saba shekara-shekara, Shugaba Buhari zai sake shillawa birnin Landan ganin Likita
  • Da farko zai fara zuwa kasar Kenya don halartan wani taro daga nan kuma ya tafi Landan inda zai kwashe makonni 2
  • Tun bayan ciwon kunnen da yace yana fama da shi, har yanzu yan Najeriya basu san abinda Buhari ke zuwa Landan ba

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari zai tafi Landan, kasar Birtaniya, don ganin Likitocinsa na tsawon makonni biyu bayan halartan taron majalisar dinkin duniya da za'ayi a Kenya.

Mai magana da yawun Shugaban kasa, Femi Adesina, ya tabbatar da hakan a jawabin da ya saki ranar Talata.

Ya ce:

"Shugaba Buhari zai tashi daga Abuja yau Talata 1 ga Maris don halartan murnar cika shirin majalisar dinkin duniya na yanayi shekaru 50 (UNEP@50), da aka shirya yi ranar 3-4 ga Maris, 2022, a Nairobi, Kenya, sakamakon gayyatar da takwararsa na Kenya, Uhuru Knyatta yayi masa."

Kara karanta wannan

Mun yi ittifaki, Wajibi ne wanda zai gaji Buhari ya kasance Kirista daga kudancin Najeriya: CAN

Shugaba Buhari
Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari zai tafi birnin Landan ganin Likita na tsawon makonni 2 Hoto: Presidency
Asali: Facebook

Adesina yace Shugaba Buhari zai samu rakiyar Ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama; Karamar ministar yanay, Sharon Ikeazor; NSA Manjo Janar Babagana Monguno; DG na NIA, Ambasada Rufai Abubakar, da Shugabar hukumar yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa.

Ya kara da cewa Buhari zai gabatar da jawabi a taron.

Asali: Legit.ng

Online view pixel