Babu ruwana: Babban sakataren gwamnatin Katsina ya karyata cewar yana da hannu a fashi da makami

Babu ruwana: Babban sakataren gwamnatin Katsina ya karyata cewar yana da hannu a fashi da makami

  • Sakataren gwamnatin Katsina, Mustapha Inuwa ya karyata zargin cewa yana da alaka da yan fashi da makami da suka addabi jihar
  • Inuwa ya ce babu yadda za a yi ya kasance cikin matsalar alhalin yana tare da masu neman mafita me dorewa kan lamarin, inda ya ce ko shi yan bindiga sun yi garkuwa da yan uwansa
  • Ya bayyana hakan ne yayin da yake sanar da aniyarsa ta yin takarar kujerar gwamnan jihar a zabe mai zuwa

Katsina - Babban sakataren gwamnatin jihar Katsina, Dr Mustapha Inuwa, ya nesanta kansa daga samun kowace alaka da yan bindiga da rashin tsaro a jihar.

Inuwa ya yi karin hasken ne yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a ranar Laraba, 16 ga watan Maris, a Katsina bayan ya ayyana aniyarsa ta yin takarar gwamna a zabe mai zuwa, The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Shawaran Masari ga masu rike da mukamai: Ku ajiye mukamanku kafin takara

Babu ruwana: Babban sakataren gwamnatin Katsina ya karyata cewar yana da hannu a fashi da makami
Babu ruwana: Babban sakataren gwamnatin Katsina ya karyata cewar yana da hannu a fashi da makami Hoto: The Nation
Asali: UGC

Ya gabatar da wasika don sanar ma shugabancin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na jihar kudirinsa.

Inuwa ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu daga cikin yan uwana.

“Idan ina da hannu a lamarin rashin tsaro, da ba a yi garkuwa da yan uwana ba.

“Sai da na sadaukar da rayuwata a kan wannan lamari na rashin tsaro. Na ziyarci yan bindiga duk da sunan neman mafita mai dorewa kan wannan matsalar.

“Na hau babur domin ganawa da shugabanninsu. Na fada masu cewa zan zauna tare da su a sansaninsu, a bari shugabansu ya je ya tattauna da Gwamna Aminu Masari.

“Na fada masu cewa idan shugabansu ya dawo, sai su barni na wuce, sannan idan bai dawo ba, su yi mani duk abun da aka yi masa.

Ya yi bayanin cewa babu dalilin da zaisa ya kasance cikin matsalar alhalin yana daga cikin mutanen da ke kokarin neman mafita me dorewa, rahoton Daily Nigerian.

Kara karanta wannan

Katsina: Yan bindiga sun bude wuta a kan wata mota, sun kashe fasinjoji 5

Shawaran Masari ga masu rike da mukamai: Ku ajiye mukamanku kafin takara

A gefe guda, mun kawo a baya cewa Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya bukaci masu rike da mukaman siyasa, wadanda ke da ra’ayin yin takarar mukaman gwamnati a 2023, da su bi tanade-tanaden dokar zabe.

Gwamnan ya yi kiran ne a ranar Talata, 15 ga watan Maris, a Katsina yayin da yake zantawa da manema labarai bayan wata ganawar sirri tare da masu rike da mukaman siyasar, PM News ta rahoto.

Taron ya kuma samu halartan mataimakinsa, Alhaji Mannir Yakubu, rahoton The Punch.

Asali: Legit.ng

Online view pixel