Bacin zuciya: Kotu ta yankewa malamin addini hukuncin kisa bayan ya kashe amininsa

Bacin zuciya: Kotu ta yankewa malamin addini hukuncin kisa bayan ya kashe amininsa

  • Babbar kotu da ke zama a Tafawa Balewa Square ta yankewa wani malamin addini hukuncin kisa kan kashe abokinsa tare da yanka gawarsa
  • Mai shari’a Modupe Nicol-Clay ce ta yankewa malamin mai suna Fatai Afobaje hukuncin bayan ta same shi da laifi dumu-dumu
  • Ya aikata laifin ne a ranar 13 ga Fabrairu, 2015, a kauyen Itire Magbon da ke Badagry, jihar Legas

Lagos - Wata b

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ya rahoto cewa Mai shari’a Modupe Nicol-Clay ta yankewa malamin hukuncin kisa bayan ta same shi da laifin hada baki da shi wajen aikata kisan kai.

Mai shari’ar ta bayyana cewa gwabbar kotu da ke zama a Tafawa Balewa Square a ranar Laraba, 16 ga watan Maris, ta yankewa wani malamin addini mai shekaru 34, Fatai Afobaje, hukuncin kisa kan kashe abokinsa tare da yanka gawarsa.amnatin jihar Lagas, wacce ta shigar da karar, ta kafa hujja fiye da tunani.

Kara karanta wannan

Takara a 2023: Ɗiyar Bola Tinubu ta yi tsokaci kan shirin mahaifinta na gaje kujerar Buhari

Bacin zuciya: Kotu ta yankewa malamin addini hukuncin kisa bayan ya kashe amininsa
Bacin zuciya: Kotu ta yankewa malamin addini hukuncin kisa bayan ya kashe amininsa Hoto: Thisday
Asali: UGC

Nicol-Clay ta bayyana cewa mai karar yay i nasarar tabbatar da cewar wanda ake karar ne ya haddasa mutuwar abokinsa, Rafiu Sulaiman, mai shekaru 44.

NAN ya ruwaito cewa an tsare wanda ake karar tun bayan da aka gurfanar da shi a 2017, wanda a lokacin ya ki amsa laifinsa.

Tawagar masu kara, karkashin jagorancin Misis Adesola Adekunle-Bello, ta kira shaidu shida sannan ta gabatar da wasu shaidu 12 a yayin shari’ar.

Masu gabatar da kara sun shaida wa kotun cewa wanda ake tuhumar ya kashe Sulaiman ne tare da yanke masa kai, hanji, huhu, dawa da hannaye.

Ya ce lamarin ya faru ne a ranar 13 ga Fabrairu, 2015, a kauyen Itire Magbon da ke Badagry, jihar Legas.

Laifukan sun ci karo da sashe na 221 da 231 na dokar laifuka ta jihar Legas, na 2011.

Kara karanta wannan

Auran Sarauta: Sarkin Iwo zai angwance da jikar Sarkin Kano Ado Bayero, Firdausi

Kotu ta yi watsi da ikirarin Abdulmalik Tanko cewa ba shi ya kashe Hanifa ba

A wani labari na daban, babbar Kotun jihar Kano ta fara shirin yanke hukunci game da shari'ar kisan Hanifa Abubakar yar kimanin shekara biyar a duniya, kamar yadda Aminiya ta ruwaito.

Kotun ta yi watsi da ikirarin wanda ake zargi na farko, Abdulmalik Tanko, wanda ya canza maganarsa ta farko, inda ya ce ba shi ne ya kashe Hanifa ba.

Rahoto ya nuna cewa yanzu haka, Kotun ƙarkashin jagorancin mai shari'a Usman Na’abba, na shirin yanke hukunci kan kisan daliba Hanifa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel