Da Dumi-Dumi: Kotu ta yi watsi da ikirarin Abdulmalik Tanko cewa ba shi ya kashe Hanifa ba

Da Dumi-Dumi: Kotu ta yi watsi da ikirarin Abdulmalik Tanko cewa ba shi ya kashe Hanifa ba

  • Babbar Kotun Kano ta yi watsi da ikirarin shugaban makarantar su Hanifa Abubakar, Abdulmalik Tanko
  • Tanko, wanda da farko ya amsa cewa ya kashe Hanifa, ya bukaci Kotu ta yi watsi da maganarsa domin ya faɗeta ne don tsirar da rayuwarsa
  • Sai dai alkalin Kotun, Mai Shari'a Usman Na’abba, ya ce bai gamsu da hujjojin Tanko ba, dan haka ya karbi cewa ba'a tursasa masa ba

Kano - Babbar Kotun jihar Kano ta fara shirin yanke hukunci game da shari'ar kisan Hanifa Abubakar yar kimanin shekara biyar a duniya, kamar yadda Aminiya ta ruwaito.

Kotun ta yi watsi da ikirarin wanda ake zargi na farko, Abdulmalik Tanko, wanda ya canza maganarsa ta farko, inda ya ce ba shi ne ya kashe Hanifa ba.

Kara karanta wannan

Kayar Kifi tayi ajalin DIG Egbunike, babban dan sandan dake binciken Abba Kyari

Rahoto ya nuna cewa yanzu haka, Kotun ƙarkashin jagorancin mai shari'a Usman Na’abba, na shirin yanke hukunci kan kisan daliba Hanifa.

Abdulmalik Tanko
Da Dumi-Dumi: Kotu ta yi watsi da ikirarin Abdulmalik Tanko cewa ba shi ya kashe Hanifa ba Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Alƙalin Kotun na shirin yanke hukunci ne bayan gamsuwa da cewa babu wanda ya tilasta wa wanda ake zargi, shugaban makaranta, Abdulmalik Tanko, ya amince shi ya kashe yarinyar.

Tun da farko Tanko ya roki Kotun ta yi watsi da kalamansa na farko da ya amsa kisan Hanifa, ya kuma kafa hujja da cewa ya yi haka ne domin ceton rayuwarsa daga azabtarwan yan sanda.

Yayin zaman cigaba da sauraron ƙarar, Tanko ya shaida wa Kotu yadda yan sanda suka rinka azabtar da shi kuma suka masa barazanar kisa matukar bai amsa laifin da ake tuhumarsa ba.

Sai dai bayanan Tanko ya saɓa wa na matar da ake zargin su tare, Fatima Jibrin, wacce ta bayyana cewa masu binciken sun ba ta tsoro amma ba su doke ta ba.

Kara karanta wannan

An tasa keyar dan adawan Ganduje, Dan Bilki Kwamanda, gidan gyara hali

A nasu bangare, yan sandan da suka gudanar da bincike sun musanta zargin Tanko, tare da faɗa wa Kotu cewa sun bi hanyoyin da ya dace wajen karban bayanan mutanen da ake zargin.

Kotu ta yi watsi da ikirarin Tanko

Mai Shari'a Na'abba, ya yi watsi da ikirarin Tanko, inda yace bai kawo hujjojin da zasu gamsar da Kotu cewa an tursasa masa ba wajen bincike.

Vanguard ta rahoto Alƙalin ya ce:

"Na gamsu cewa an bi hanyoyin da ya dace wajen karɓan bayanan mutum biyu na farko da ake zargi kuma da yardarsu, saboda haka na karbi bayanan."

A wani labarin na daban kuma Kwankwaso ya yi babban Kamu a Kano, wasu shugabannin PDP sun yi murabus, za su koma NNPP

Wasu kusoshin jam'iyyar PDP a karamar hukumar Rano ta jihar Kano sun yi murabus daga kan mukamansu da nufin bin Kwankwaso.

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, yace zai bar PDP kafin karshen watan Maris, alamu sun nuna zai koma NNPP.

Kara karanta wannan

Rashawa: Shugaban EFCC ya goyi bayan maganar Obasanjo kan masu son gaje kujerar Buhari a 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel