Auran Sarauta: Sarkin Iwo zai angwance da jikar Sarkin Kano Ado Bayero, Firdausi

Auran Sarauta: Sarkin Iwo zai angwance da jikar Sarkin Kano Ado Bayero, Firdausi

  • Bayan shekara biyu da mutuwar aurensa, Sarkin Iwo zai sake shiga daga ciki da jikar Sarkin Kano
  • Rahoto ya nuna cewa za'a yi bikin daurin auren ne ranar 19 ga maris 2022
  • A baya wasikun Sarkin sun bayyana yadda ake neman kudi N20m wajen gwamnati don wannan aure

Bayan rabuwa da matarsa yar kasar Jamaica a shekarar 2019, Oluwo of Iwo ya gamu da sabuwar soyayya a kasar Kano.

Sarkin kasar Iwo ta jihar Osun, Adewale Akanbi (Telu 1), na gab da angwancewa da yar Sarki, Firdauz Abdullahi a jihar Kano.

An shirya auren ranar 19 ga Maris, 2022, a gidan Madakin Kano, rahoton Premium Times.

Sarkin Iwo
Auran Sarauta: Sarkin Iwo zai angwance da jikar Sarkin Kano Ado Bayero, Firdausi
Asali: Original

Kara karanta wannan

An tasa keyar dan adawan Ganduje, Dan Bilki Kwamanda, gidan gyara hali

A ranar Talata, wata majiyar fadar Sarki ta bayyana cewa yar Sarkin kyakkyawar budurwa ce yar shekara 27.

Majiyar ta kara da cewa jikar Sarki Ado Bayero ce.

Oba Adewale ya shahara da yaki da masu ikirarin addinin gargajiya a kasar Yarbawa.

A jawaban da yayi lokaci bayan lokaci, ya jaddada cewa Allah daya yake bautawa kuma bai bautawa gumaka kamar yadda al'ada ta bukata.

Hakazalika Sarkin na fito-na-fito da yan damfara yahoo-yahoo masu asiri don samun kudi.

Takardar ta nuna cewa sarkin yana bukatar kudi don yin gagarumin bikin

Daily Trust ta ruwaito yadda fadar Oluwo ta saki wannan takardar ne bayan wata takarda ta dinga yawo a kafafen sada zumunta wacce ta nuna basaraken yana bukatar N20m daga gwamnatin jihar don ya auri Gimbiyar Kano.

Hadimin gwamnan na musamman akan harkar sarauta ne ya amshi takardar a maimakon gwamnan mai kwanan wata 8 ga watan Fabrairun 2022 wacce aka tura wa Oyetola.

Kara karanta wannan

Yanzu: Bayan Shan Matsin Lamba Daga Mata, Majalisa Ta Canja Ra'ayinta Kan Dokar Mata, Za Ta Sake Sabon Kuri'a

Kamar yadda wani bangaren takardar yazo:

“Mai mataba Oba (Dr) Abdulrasheed Adewale Akanbi, Oluwa na kasar Iwo ya ba ni umarnin sanar da kai cewa Oluwo zai auro gimbiya daga masarautar Kano, diyar Ado Bayero. Ina farin cikin sanar da gwamna cewa bikin da zai hada masarautun guda biyu yana bukatar kashe dukiya mai yawan gaske. Hakan yasa muke neman tallafi daga gwamnatin jihar nan.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel