An Gurfanar Da Makaniken Da Ya Sayar Da Motar Kwastomansa a Kaduna

An Gurfanar Da Makaniken Da Ya Sayar Da Motar Kwastomansa a Kaduna

  • Wani bawan Allah a Kaduna ya yi karar wani makanike saboda zarginsa da sayar masa da mota kirar Honda Accord
  • Makaniken da aka yi kara a kotu, Stanley Collins, dan shekara 30 ya musanta zargin da ake masa
  • Lauyan wanda ya shigar da karar ya shaida wa kotu cewa Collins ya sayar da motar ne kan N980,000 amma ya yi ikirarin cewa an sace ne

Kaduna - An gurfanar da wani makanike mai shekaru 30, Stanley Collins, a ranar Laraba, a gaban kotun majistare da ke Kaduna kan zarginsa da sayar da motar kwastomansa kirar Honda Accord kan kudi N980,000.

An tuhumar wanda aka yi karar, mazaunin Kaduna, da aikata laifin sata, rahoton Daily Nigerian.

Amma, Collins, ya musanta laifin da ake tuhumarsa da aikatawa.

An Gurfanar Da Makaniken Da Ya Sayar Da Motar Kwastomansa
An Gurfanar Da Makaniken Da Ya Sayar Da Motar Kwastomansa a Kaduna. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Layan wanda ya shigar da kara ya yi wa kotu bayanin yadda aka sace motar

Kara karanta wannan

Kano: NSCDC Ta Kama Wani Mutum Da Katin Waya 22 Da Katin ATM 14

Lauyan wanda ya shigar da kara, Sifeta Chidi Leo, ya shaida wa kotu cewa wanda aka yi karar ya aikata laifin ne a ranar 10 ga watan Fabrairu misalin karfe 10 na dare a Kabala West, Kaduna.

Ya yi zargin cewa wanda aka yi karar ya sace wata Honda Shuttle, mallakar Mr Gabriel Paul, wanda ya kai masa gyara.

Leo ya ce wanda aka yi karar ya sace motar ya sayarwa wani mutum daban yayin da ya yi ikirarin wani ya sace motar cikin dare.

Wanda ya shigar da karar ya shaida wa kotu an gano motar daga hannun wanda aka sayarwa ta hanyar amfani da tracker.

Ya ce laifin ya ci karo da sashi na 287 na Penal Code na Jihar Kaduna, 2017.

Kotu ta bada belin wanda aka yi karar kan N200,000

Kara karanta wannan

2023: Wani Ɗan Kasuwa Mazaunin Abuja Ya Shiga Jerin Masu Neman Gadon Kujerar Buhari a APC

Alkalin kotun, Ibrahim Emmanuel, ya bada belin wanda ake zargin kan kudi N200,000 da mutane biyu da suka tsaya masa.

Mr Emmanuel ya bada umurnin cewa mutanen biyu da za su karbi belin wanda ake zargin su kasance masu aiki sannan su nuna shaidan biyan haraji ga gwamnatin Kaduna.

Ya dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 12 ga watan Afrilun 12.

An sha mamaki bayan gano cewa gardin namiji aka tura gidan yari na mata ba tare da an gane a kotu ba

A wani labarin, wani lamari mai ban mamaki ya auku a gidan gyaran halin mata da ke Shurugwu a makon da ya gabata, inda aka gano wata fursuna ba mace bace, katon namiji ne kamar yadda LIB ta ruwaito.

Praise Mpofu mai shekaru 22 ya na sanye da suturar mata ne a lokacin da aka kama shi inda ya bayyana kamar karuwa don ya yaudari maza ya yi musu sata.

Kara karanta wannan

Sata kamar Bera: Tsabar satarsa tasa mahaifinsa ya mutu, ya sake tafka sata a wajen jana'izarsa

An kama Mpofu ne bayan ya yi wa wani mutum da ke yankin Gweru sata. An samu rahoto akan yadda mutumin ya caskewa Mpofu kudi don su kwana tare da shi a tunanin sa mace ne, daga nan Mpofu ya yashe shi ya tsere.

Asali: Legit.ng

Online view pixel