Sata kamar Bera: Tsabar satarsa tasa mahaifinsa ya mutu, ya sake tafka sata a wajen jana'izarsa

Sata kamar Bera: Tsabar satarsa tasa mahaifinsa ya mutu, ya sake tafka sata a wajen jana'izarsa

  • An tuhumi wani korarren dan sanda John Dennis da satar karfen da kudinsa ya kai N6,000 a ranar da aka binne mahaifinsa da ya mutu
  • Kotun Majistare ta Ebute-Meta ta yankewa dan sandan mai shekaru 36 hukuncin daurin watanni 27 a gidan yari
  • A halin da ake ciki kuma, an ce halinsa na sata ne ya yi sanadiyyar mutuwar mahaifinsa wanda shi ma mataimakin Sufeton ‘yan sanda ne mai ritaya

Kotun Majistare ta Ebute-Meta da ke Legas ta yanke hukuncin daurin watanni 27 ga wani korarren dan sanda, John Dennis, mai shekaru 36 da haihuwa.

An yanke masa hukuncin ne bisa laifin satar wani karfe, wanda kudinsa ya kai N6,000 a ranar da aka binne mahaifinsa da ya mutu, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

An yankewa barawon rodi hukuncin watanni a gidan yari
Sata kamar Bera: Tsabar satarsa ubansa ya mutu, ya sake tafka sata a wajen jana'iza | Hoto: punchng.com
Asali: Twitter

Da kansa ya amsa laifnsa

Alkalin kotun, Misis Folarin Williams ta ce:

“Wanda ake tuhumar ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi kuma ya amsa laifin da ya aikata. Ya ce ya yi niyyar sayar da karfen rodin da ya sace a ranar da za a binne mahaifinsa.
“Abin sha'awa shi ne cewa babu wata shaida mai nauyi kamar ta ikirarin wanda ake tuhuma.
“Mai shigar da kara, ASP Cousin Adams, yayin da yake shaida gaskiyar lamarin ya ce an gurfanar da wanda ake kara a kusan dukkanin kotuna da ke Ebute-Meta bisa aikata irin wannan laifin.
“Ya ce saboda laifukan da ya aikata an kore shi daga aikin ‘yan sanda, inda ya kara da cewa halinsa na sata ne ya yi sanadin mutuwar mahaifinsa, wanda kuma shi ma mataimakin Sufeton ‘yan sanda ne mai ritaya.

A cewar dan sandan, ya aikata laifin ne a gaban ofishin ‘yan sanda na Denton, kan titin Murtala Muhammed da ke Ebute-Meta a Legas.

Adams ya ce Dennis ya saci karafan rodi guda hudu da kudinsu ya kai N6000, mallakin kamfanin STEEP Development Company Limited.

Jami'an tsaro sun kama wani kasurgumin mai garkuwa da mutane bayan sace matar aure a jigawa

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta kama wani mutum mai shekaru 46 da ake zargi da yin garkuwa da mutane a karamar hukumar Kirikasamma da ke jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda (PPRO) na rundunar, ASP Lawan Shiisu, ya tabbatar da hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a Dutse ranar Talata.

Shiisu ya ce wanda ake zargin da aka kama a ranar 28 ga watan Fabrairu, ana zargin dan tawagar da suka yi garkuwa da wata yarinya ‘yar shekara 22, Hadiza Alhaji-Chadi kwanan nan a kauyen Marma.

A cewar Shiisu:

“Ta hanyar bayanan sirri, rundunar ta samu nasarar cafke wani mai suna Ado Ahmadu mai shekaru 46 kuma mazaunin Marawaji a karamar hukumar Kirikasamma bisa laifin yin garkuwa da mutane."

Kun kyauta: Amurka ta taya EFCC murnar kama mai laifin da FBI ta dade tana nema

A wani labarin, Gwamnatin Amurka ta taya hukumar EFCC murnar kama wani dan Najeriya da ke cikin jerin sunayen wadanda hukumar FBI ke nema ruwa a jallo bisa zarginsa da laifin zamba da ya kai dala miliyan 100, da karkatar da kudade, da kuma satar bayanan sirri.

Hukumar EFCC, a cikin wata sanarwa a ranar Litinin, ta sanar da kama mutumin, Osondu Victor Igwilo, a wani dakin taro da ke unguwar Sangotedo a Legas, a yankin Kudu-maso-Yammacin Najeriya.

Rahoton Premium Times ya ce an kama Mista Igwilo mai shekaru 42 a ranar 11 ga Maris, tare da Okafor Nnamdi Chris, Nwodu Uchenna Emmanuel da John Anazo Achukwu, kamar yadda EFCC ta bayyana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel