An sha mamaki bayan gano cewa gardin namiji aka tura gidan yari na mata ba tare da an gane a kotu ba

An sha mamaki bayan gano cewa gardin namiji aka tura gidan yari na mata ba tare da an gane a kotu ba

  • Wani lamari mai ban mamaki ya auku a gidan gyaran halin mata na Shurugwi a makon da ya gabata
  • An gano cewa ashe katon namiji ne wani Praise Mpofu da ‘yan sanda su ka kama a matsayin barauniya kuma aka yanke ma sa hukunci
  • Bincike ya nuna cewa ya na sanya suturar mata ne don ya yaudari maza a matsayin karuwa, daga nan ya sace musu dukiya

Zimbabwe - Wani lamari mai ban mamaki ya auku a gidan gyaran halin mata da ke Shurugwu a makon da ya gabata, inda aka gano wata fursuna ba mace bace, katon namiji ne kamar yadda LIB ta ruwaito.

Praise Mpofu mai shekaru 22 ya na sanye da suturar mata ne a lokacin da aka kama shi inda ya bayyana kamar karuwa don ya yaudari maza ya yi musu sata.

Kara karanta wannan

Dan achaba ya tsinta N20.8m a titi, ya samu tukuicin N600k bayan ya mayar wa masu kudin

Abin mamaki: Yadda aka gano ashe ƙaton namiji ne aka tura gidan yari na mata
An gano cewa ƙaton namiji aka kai gidan yari na mata ba tare da an sani ba. Hoto: LIB
Asali: Facebook

An kama Mpofu ne bayan ya yi wa wani mutum da ke yankin Gweru sata. An samu rahoto akan yadda mutumin ya caskewa Mpofu kudi don su kwana tare da shi a tunanin sa mace ne, daga nan Mpofu ya yashe shi ya tsere.

Kamar yadda LIB ta ruwaito, bayan kwanaki kadan da yin satar aka kama shi a wani yanki na Gweru a Mkoba 6. A lokacin da aka kama shi ya na sanye ne da sikel da riga. Ya yi kitso irin na mata sannan ya yi ciko a kirji ya sa rigar mama kamar mace.

Har a kotu ba a gane namiji bane

Har aka gabatar da shi kotun majistare da ke Gweru a matsayin barawo, be bayyana cewa shi namiji ba ne.

Kara karanta wannan

Na yi gyaran kwata ana biya na N20: Ɗan kwallo mafi tsada a Afirka kuma tauraron Super Eagles, Victor Osimhen

Sakamakon hakan kotu ta yanke ma sa hukuncin dauri a gidan gyaran hali na mata da ke Shurugwi.

Saboda wasu dalilai ba a samu damar wucewa da shi gidan gyaran halin ba, sai aka kai shi gidan kaso na wucin gadi inda ake ajiye masu laifi mata su yi kwana 2.

Sai bayan an kai shi gidan gyaran halin na Shurugwi ne asirin sa ya tonu.

Kakakin hukumar kula da gidan yari, Nevson Tagarira ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Kamar yadda ya shaida:

“Eh akwai wani da aka daure daga ZRP, ta kotun majistare ya je a matsayin mace. Sai da aka bi hanyar gane fursinoni mata sannan aka gane namiji ne ba mace ba. Daga gidan gyaran hali na mata da ke Shurugwi aka wuce da shi gidan gyaran hali na maza na Hwahwa Maximum a ranar da lamarin ya auku.”

Wata ma’aikaciyar lafiya da ke duba fursinoni mata ce ta gano cewa katon namiji ne kamar yadda wata majiya ta bayyana.

Kara karanta wannan

Mace mafi tsawo a duniya: Rumeyasa Gelgi 'yar ƙasar Turkiyya

Majiyar ta shaida cewa:

“Kwana biyu Mpofu ya yi a gidan masu kananun laifi na Gweru inda ya ki bayyana cewa shi namiji ne.
"An gano bakin zaren ne bayan an kai shi gidan gyaran halin mata na Shurugwi daga nan aka gano namiji ne, kitso ya yi sannan ya yi ciko a kirji kamar mace sannan sanye yake da buje.
"An kama shi ne a matsayin karuwar da ta yi sata bayan an biya ta kudin da za a kwana da ita.”

Magidanci Ya Lakaɗa Wa Likitan Fata Mugun Duka Saboda Yaba Kyawun Fatar Matarsa

A wani labarin daban, 'yan sanda sun kama wani mutum bayan ya lakada wa likita dukan tsiya inda ya bar shi a mawuyacin hali bayan yabon kyawun fatar matar sa.

Matar wacce musulma ce mai sanye da hijabi ta sanar da mijinta, Bakhriddin Azimov cewa likitan fatar dan asalin kasar Rasha, Vladimir Zhirnokleev ya yaba kyawun fatarta.

Kara karanta wannan

Magidanci ya kashe matarsa saboda ta raina bajintarsa wurin kwanciyar aure

Daga nan ne mutumin ya kai wa likitan farmaki, yanzu haka yana fuskantar hukunci akan cin zarafi kamar yadda LIB ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel