Kano: NSCDC Ta Kama Wani Mutum Da Katin Waya 22 Da Katin ATM 14

Kano: NSCDC Ta Kama Wani Mutum Da Katin Waya 22 Da Katin ATM 14

  • Rundunar tsaro ta fararen kaya, NSCDC, ta Jihar Kano ta kama wani Ahmad Abdulsalam da katinan waya masu rijista guda 22 da katin banki guda 14
  • Kwamandan rundunar na jihar, Adamu Zakari, ya bayyana hakan a ranar Talata da dare a cikin garin Kano inda yace hakan babbar nasara ce
  • Kamar yadda ya shaida, jami’an sun kama shi dumu-dumu inda suka nemi karin bayani inda ya bayyana musu wadanda suke taimaka masa wurin mallakar katinan

Kano - Rundunar tsaro ta NSCDC, reshen Jihar Kano, ta samu nasarar damkar wani Ahmad Abdulsalam da tsakar daren Talata da katinan waya guda 22 duk masu rijista da kuma wasu katin mutane daban-daban na banki guda 14.

Kwamandan rundunar, Adamu Zakari, ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Talata da dare cikin garin Kano, The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: Wani Ɗan Kasuwa Mazaunin Abuja Ya Shiga Jerin Masu Neman Gadon Kujerar Buhari a APC

Kano: NSCDC Ta Kama Wani Mutum Da Katin Waya 22 Da Katin ATM 14
NSCDC ta kama wani mutum da katin waya 22 Da Katin ATM 14 a Kano. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

Ya kwatanta kamen a matsayin nasara mai yawa cikin kankanin lokaci daga hawan sa mukamin.

Mutumin ya hada su da jami’in kamfanin layin wayoyi wanda yake siyar masa da katinan

Kamar yadda ya shaida bisa ruwayar The Punch:

“Jami’an mu sun kama Abdulsalam wanda ya gaza bayar da bayanai kwarara akan yadda ya mallaki katinan banki guda 14.
“Bayan ya ji ruwan tambayoyi, ya hada mu da wani Umar Surajo wanda a cewarsa shi ne asalin mai laifin. Daga nan ya shaida cewa Surajo ne ya tura shi banki don ya sanya katinan su fara aiki.
“Zakari ya tsaya akan cewa Muhammad Ali, wani ma’aikacin kamfanin layukan wayar shi ne ya samar masa da katinan. Bayan tsananta bincike ne muka gano cewa ana siyan katinan bankunan wurin ‘yan kauye ne wadanda basu san amfanin su ba.”

Kara karanta wannan

2023: Bayan Uba Sani, Kwamishina a Kaduna Ya Ce Shima Yana Son Ya Gaji El-Rufai

Su na siyan katinan banki a wurin ‘yan kauye a farashin N300

Ya ci gaba da bayyana cewa su na zuwa kauyaku ne inda suke siyan katinan bankuna a N300 ko wanne.

Kwamandan ya ja kunnen jama’a akan siyar sa katin bankin su sakamakon yadda ake amfani da su wurin yin ayyuka marasa kyau ciki har da ta’addanci, halasta kudin haram, biyan masu garkuwa da mutane da sauran su.

Ya bukaci jama’a da su yi gaggawar sanar da hukuma idan suka samu labari akan wata harka makamanciyar wannan a Kano ko kuma Najeriya gaba daya.

Katsinsa: Ɗan Shekara 22 Ya Sace Wa Dattijuwa Kuɗinta Na Garatuti Baki Daya, Ya Siya Mota Da Babur

A wani labarin, Yan sanda a Jihar Katsina, a ranar Litinin sun yi holen wani Aliyu Abdullahi mai shekaru 22, mazaunin Kasuwar Mata Street a Karamar Hukumar Funtua saboda damfarar wata tsohuwa.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban majalisar wakilan tarayyar da ya rika karbar albashin N15, 000 ya rasu

Ya wawushe mata dukkan kudinta na garatuti ta hanyar amfani da katin ta na banki wato ATM inda ya siya mota da babur da kudin, Vanguard ta ruwaito.

An taba kama mayaudarin, wanda ya kware wurin damfarar mutane ta hanyar sauya musu katinsu na ATM a baya amma daga bisani ya fito daga gidan yari kuma ya cigaba da laifin, rahoton Vanguard.

Asali: Legit.ng

Online view pixel