Da Dumi-Dumi: Muna bayan ka, Sanatocin APC sun tura sako game da takarar Tinubu a 2023

Da Dumi-Dumi: Muna bayan ka, Sanatocin APC sun tura sako game da takarar Tinubu a 2023

  • Mambobin majalisar dattawa na jam'iyyar APC sun tabbatar da goyon bayansu ga jagoran APC na ƙasa Bola Tinubu ya gaji Buhari
  • Tsohon gwamnan jihar Legas ya gana da Sanatocin APC ranar Laraba a Abuja domin neman haɗin kansu na cika burinsa
  • Ya bukaci Sanatocin su taimaka masa ya cika burinsa na zama shugaban ƙasa domin gyara Najeriya

Abuja - Mambobin jam'iyyar All Progressive Congress (APC) a majalisar dattawan Najeriya sun tabbatar wa jagora, Bola Ahmed Tinubu, cewa suna goyon bayan ya gaji Buhari a 2023.

The Nation ta rahoto cewa Tinubu ya kai ziyara majalisar dattawan Najeriya ne domin neman goyon bayan yan majalisu a kudurinsa na takarar shugaban ƙasa.

Jagoran ya gana da Sanatocin jam'iyyarsa ta APC a wani ɓangare na neman samun tikicin takarar shugaban ƙasa karkashin APC a 2023.

Kara karanta wannan

Shugabancin APC: Tsohon gwamnan Zamfara ya yi fatali da tsarin yanki, ya lale miliyan N20m na Fom

Sanatocin APC
Da Dumi-Dumi: Muna bayan ka, Sanatocin APC sun tura sako game da takarar Tinubu a 2023 Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

Yayin zaman, Tinubu ya roki yan majalisun APC su taimaka masa har ya samu tikitin takarar APC da zai ba shi damar fafatawa a zaben shugaban ƙasa 2023.

A cewarsa ya kawo kan shi Majalisar dattawa ne domin neman alfarmar yin aiki tare da kuma goyon bayan su wajen cika burinsa na zama shugaban ƙasa a 2023.

A jawabinsa ya ce:

"Ina bukatar shawarin ku da haɗin kai a wannan tafiya da na kudiri aniya. Ina rokon haɗin kai wajen cika burina na zama ɗan takarar jam'iyyar mu da kuma samun nasara a zaɓen watan Fabrairu 2023 ga dukkan yan takarar APC."
"Ba muna nufin idon mu ya rufe kan mulki ba, muna kokarin kafa gwamnati mai inganci ga ƙasar mu. Bangaren zartarwa da bangaren dokoki, tare zamu haɗu mu kafa bishiyar demokaraɗiyya wacce zata samar da walwala ga al'umma."

Kara karanta wannan

2023: Ina Neman Goyon Bayan Ku Don Cika Burin Rayuwa Ta, Tinubu Ga Sanatocin APC

Muna tare da kai - Sanatocin APC ga Tinubu

Da yake martani, shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya ce:

"Ranka ya daɗe, dukkan mu muna maka fatan alkairi, muna maka fatan sa'a, muna maka fatan nasara da kuma sauran harkokin ɗaga APC ta cigaba da mulkin Najeriya."
"A bayyane kuma a takaice, ranka ya daɗe muna tabbatar maka muna tare da kai."

A wani labarin na daban kuma Dan majalisa da Shugabannin APC na tsagin Ministan Buhari sun sauya sheƙa daga jam'iyyar APC

Wasu shugabannin APC na tsagin ministan yaɗa labarai, Alhaji Lai Muhammed, sun tabbatar da ficewarsu daga APC.

Sakataren kuɗi na tsagin, Tajuddeen Mohammed, ya ce a halin yanzun ba su yanke jam'iyyar da zasu koma ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel