Shugabannin APC na tsagin Ministan Buhari sun sauya sheƙa daga jam'iyyar APC

Shugabannin APC na tsagin Ministan Buhari sun sauya sheƙa daga jam'iyyar APC

  • Wasu shugabannin APC na tsagin ministan yaɗa labarai, Alhaji Lai Muhammed, sun tabbatar da ficewarsu daga APC
  • Sakataren kuɗi na tsagin, Tajuddeen Mohammed, ya ce a halin yanzun ba su yanke jam'iyyar da zasu koma ba
  • Daga cikin waɗan nan mambobi da suka ɗauki wannan matakin, har da ɗan majalisa a majalisar dokokin jihar Kwara

Kwara - Wasu mambobin jam'iyyar APC reshen jihar Kwara dake goyon bayan Ministan yaɗa labaru, Alhaji Lai Muhammad, sun fice daga cikin jam'iyya mai mulki.

Sakataren Kuɗi na tsagin ministan, Tajudeen Mohammed, shi ne ya tabbatar da haka ga jaridar Daily Trust a wata fira ta wayar salula.

Alhaji Lai Muhammed
Shugabannin APC na tsagin Ministan Buhari sun sauya sheƙa daga jam'iyyar APC Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A jawabinsa, Muhammed ya ce:

"Ina mai tabbatar muku da cewa mun fice daga jam'iyyar APC. Duk da har yanzu ba mu yanke inda muka dosa ba, amma muna cigaba da shawari domin gano jam'iyyar da ta dace da mu."

Kara karanta wannan

Jirgin yakin NAF ya yi luguden wuta a wurin shagalin auren kasurgumin ɗan bindiga, rayuka sun salwanta

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dan majalisa ya bi sahu

Rahoto ya nuna cewa daga cikin waɗan nan fusatattun mambobin, har da ɗan majalisa a majalisar dokokin jihar Kwara, Honorabul Saheed Popoola, wanda shi ma ya fice daga APC.

Wannan shi ne karon farko da wani mamba da ya balle daga jam'iyya a jihar, ya fice tun farkon lokacin da APC ta samu ɓaraka a reshen jihar Kwara.

A hasashen masana harkokin siyasa, wannan lamarin ya buɗe wa sauran mambobin dake ganin an musu ba dai-dai ba ƙofar fice wa daga jam'iyya.

Honorabul Popoola, ɗan gani kashenin ministan yaɗa labarai da al'adu, Alhaji Lai Muhammed ne, kuma ministan ne jagoran tsagin APC da ga ɓalle a Kwara.

A wani labarin na daban kuma Tsagin Mala Buni ya kwace ikonsa a Hedkwatar APC, ya faɗi gaskiyar abun da ya faru

Kara karanta wannan

Jerin yadda Sojoji 18, yan sanda 6 da yan Najeriya 76 suka rasa rayukansu cikin mako daya

Kwamitin rikon kwarya karkashin jagorancin Gwamna Buni na Yobe ya sake dawo da ƙarfinsa a hedkwatar APC ta ƙasa.

Sakataren kwamitin na kasa, Sanata Akpanudoedehe, ya koma bakin aiki bayan jita-jitar ya yi murabus ko an canza shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel