Jita-jita kan yajin 'yan sanda: IGP ya ba da umarnin aiwatar da sabon tsarin albashin 'yan sanda

Jita-jita kan yajin 'yan sanda: IGP ya ba da umarnin aiwatar da sabon tsarin albashin 'yan sanda

  • Sufeto janar na 'yan sandan Najeriya ya ba da umarnin aiwatar da sabon tsarin albashin 'yan sanda a kasar nan
  • Wannan na zuwa ne jim kadan bayan da aka yada jita-jitar wasu jami'ai na shirin fadawa yajin aiki saboda karancin kayan aiki
  • An gargadi jami'an tsaron da su guji fadawa yajin aiki, kuma an nemi a wayar da kan jami'ai kan wannan lamari

Abuja - Ga dukkan alamu hukumomin rundunar ‘yan sandan Najeriya na daukar matakai don dakile yajin aikin da ake yayatawa ma’aikatanta za ta shiga ta hanyar ba da umarnin aiwatar da sabon tsarin albashi cikin gaggawa.

Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya Usman Alkali Baba, ya kuma amince da rabon kayan sawa na aiki da sauran kayan aiki ga jami’an 'yan sanda, Ripples Nigeria ta ruwaito.

Kara karanta wannan

IGP ya bayyana dalilin da yasa jami’an yan sanda basu samu karin albashi ba har yanzu

Albashin 'yan sanda zai inganta nan kusa
Jita-jita kan yajin 'yan sanda: IGP ya ba da umarnin aiwatar sabon albashin 'yan sanda | Hoto:premiumtimesng.com
Asali: Facebook

A farkon makon ne dai aka yayata jita-jitar cewa wasu ‘yan sanda na shirin shiga yajin aikin saboda rashin aiwatar da sabon tsarin albashin ‘yan sanda, gazawa wajen samar da nagartattun makamai na yaki da miyagun laifuka da kuma rashin kula da jin dadin jami’an.

Tun da farko hedkwatar rundunar ta karyata wannan jita-jita, inda ta ce bayanan da ake ta yayatawa na yajin aikin na bogi ne kuma na zunzurutun karya.

Matakan da IGP ya dauka

Ko ma dai yaya ne, sufeto janar na 'yan sanda na daukar matakan gaggawa don dakatar da shirin yajin aikin da ake zargin jami'an za su shiga, rahoton SaharaReporters.

A cewar wani sako mai kwanan wata 15 ga Maris, 2022, mai lamba, CB: 4001/DOPS/FHQ/ABJ/Vol, an gaya wa shugabannin ma’aikatun 'yan sanda da kwamishinonin ‘yan sanda na jihohi da su wayar da kan jami’ansu kan dalilan da za su sa su guji fadawa yajin aiki.

Kara karanta wannan

Jerin yadda Sojoji 18, yan sanda 6 da yan Najeriya 76 suka rasa rayukansu cikin mako daya

Hedikwatar rundunar a cikin sakon ta tabbatar da cewa babban sufeton ‘yan sanda na kasa Usman Alkali Baba ya bayar da umarnin a fara lissafin albashin a cikin sabon tsarin albashi na 'yan sanda.

Sakon ya ce:

“Rahotanni na sirri da Sufeto Janar na ‘yan sanda ke samu sun nuna cewa wasu daga cikin jami’an tsaro na shirin shiga yajin aiki saboda rashin biyan sabon tsarin albashin ‘yan sanda, gazawa wajen samar da nagartattun makamai don yaki da miyagun laifuka da kuma rashin kula da jin dadin ‘yan sanda.
"Ku sani cewa Sufeto Janar na 'yan sanda ya ba da umarnin a fara lissafa albashin nan da nan a karkashin sabon tsarin albashi, rage/cire haraji ga jami'ai don aiwatarwa cikin gaggawa, rarraba kayan aiki tare da wanda an riga an kammala a hedkwatar rundunar."

Mukaddashin jami’in hulda da jama’a na rundunar, Muyiwa Adejobi, ya gargadi jami’an hukumar cewa duk wani yajin aiki ko kawo cikas ga jami’an tsaro za a dauki su a matsayin cin amanar aiki.

Kara karanta wannan

Kungiyar ASUU ta cigaba da yajin-aiki, za a kara wasu watanni ba a bude jami’o’i ba

An hada mu fada da iyalai da 'yan uwanmu

Legit.ng Hausa ta tattauna da wani jami'in dan sandan da ya kai matsayin insfecta, wanda ya nemi a sakaya sunansa, inda ya ce batun sabon tsarin albashinsu tun farko kawai fada ya jawo musu a idon 'yan uwansu.

Ya bayyana mana cewa, an sanarwa duniya sun samu kari a albashi da kuma ingancin kayan aiki amma babu ko daya.

A cewarsa:

"Gaskiya ba a mana daidai ba, saboda wadanda ke karkashina gani suke na samu karin albashi, amma a gaskiyar lamari bamu ga komai, ku fada wa duniya.
"Mu muke kare al'umma, amma ba a bamu kudi ba, muna fama da talauci dole ka ga wasun mu suna karbar kudi a hannun mutane a wulakance, ba wai ni ina yi bane fa."

IGP ya bayyana dalilin da yasa jami’an yan sanda basu samu karin albashi ba har yanzu

A wani labarin, sufeto Janar na yan sanda, Usman Baba, ya bayyana cewa masu ruwa da tsaki da za su aiwatar da Karin albashin jami’an rundunar suna nan suna aiki kan sabon albashin har yanzu kuma za su tabbatar da faruwar hakan.

Kara karanta wannan

Gudun tsira: Mutune sun mutu garin gudun tsira a wani kauyen Katsina

Baba ya ce wannan karin kudiri ne na shugaban kasa Muhammadu Buhari ba tare da wata bukata daga ‘yan sanda ba.

Ya kuma bayyana cewa jami’an yan sandan na sane da cewa babban tashin hankali ne a tsara duk wani abin da zai kawo cikas ga lamarin tsaro balle a aiwatar da shi, Daily Trust ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel