Gudun tsira: Mutune sun mutu garin gudun tsira a wani kauyen Katsina

Gudun tsira: Mutune sun mutu garin gudun tsira a wani kauyen Katsina

  • Al'umman garin Shimfida da ke karamar hukumar Jibia, ta jihar Katsina sun tarkata yanasu-yanasu sun bar yankin
  • Hakan ya kasance ne sakamakon zargin cewa rundunar sojoji ta kwashe dakarunta daga yankin
  • An tattaro cewa mutane shida sun mutu a yayin gudun tsiran domin gujewa hare-haren yan bindiga

Katsina - Akalla mutane shida wadanda yawancinsu yara ne suka mutu yayin da mazauna garin Shimfida da ke karamar hukumar Jibia, ta jihar Katsina suke tserewa daga yankin.

An tattaro cewa mutanen na barin yankin ne kan abun da suka kira da ‘janye jami’an sojoji ba tare da sanarwa ba.’

Wannan mummunan ci gaba ya yi sanadiyar da mutanen yankin da dama ke sauya waje saboda tsoron hare-hare daga yan bindiga, Daily Trust ta rahoto.

Gudun tsira: Mutune sun mutu garin gudun tsira a wani kauyen Katsina
Gudun tsira: Mutune sun mutu garin gudun tsira a wani kauyen Katsina Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Mazauna yankin sun bayyana cewa motocin sojoji sun shigo yankin a daren ranar Laraba, sannan suka kwashe dukka jami’an sojin daga wuraren da suke na tsawon lokaci.

Kara karanta wannan

Nasrun Minallah: Gwarazan yan sanda sun kama yan bindiga 200, yan fashi 20 a jihar Kaduna

Garin Shimfida na a gefen dajin Dumburum inda anan ne aka ce manyan ‘yan fashi da makami dake ta’asa a jihohin Zamfara da Katsina suke buya.

Ya ce:

“Da sojojin sai su bamu sanarwa na akalla kwanaki biyar domin mu bar wajen, amma abun bakin ciki sai kwatsam suka zo suka kwashe mutanensu sannan suka barmu a hadarin yan bindiga.
“A yanzu da nake magana, maza da mata, tsofaffi da yara duk suna gudun tsira daga yankin kuma tuni aka tsinci gawarwakin yara shida a hanya.”

Wani mazaunin yankin ya ce ya zama masu dole su gaggauta barin garin saboda yan bindiga suna fushi da al’umman Shimfida saboda kasancewar jami’an sojoji a wajen.

Yunkurin samun martani da dalilin janye sojojin daga rundunar a Katsina ya ci tura.

Kara karanta wannan

Yadda aka yi ram da miyagun masu garkuwa da mutane a dajin Kwara

Rahoton ya kuma ce a bangaren shi, kakakin yan sanda a Katsina, SP Gambo Isah, ya ce:

“Idan sojoji sun janye jami’ansu, sune za su yi magana a kan dalilin, ba yan sanda ba.”

Yan bindiga sun yi takansu yayin da jami'an tsaro suka far musu a jihar Katsina

A wani labarin, dakarun yan sanda sun dakile harin yan bindiga kuma suka kwato Babura 6 a ƙauyen Barawa dake ƙaramar hukumar Batagarawa, jihar Katsina.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, SP Gambo Isa, shi ne ya shaida wa manema labarai haka ranar Talata a Katsina, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

A cewarsa, Yan bijilanti ne suka fara ganin tawagar yan ta'addan da adadi mai hawa haye kan Babura kuma ɗauke da AK47 nan take suka sanar da yan sanda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel