IGP ya bayyana dalilin da yasa jami’an yan sanda basu samu karin albashi ba har yanzu

IGP ya bayyana dalilin da yasa jami’an yan sanda basu samu karin albashi ba har yanzu

  • Sufeto janar na yan sandan Najeriya ya magantu a kan tsaiko da aka samu wajen aiwatar da sabon albashin jami’an rundunar
  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da yiwa jami’an yan sanda karin albashi da kaso 20 a shekarar 2021
  • Ya kamata sabon albashin ya fara aiki a watan Janairun 2022, sai dai kuma, watanni uku bayan haka, ba a aiwatar da shi ba

Sufeto Janar na yan sanda, Usman Baba, ya bayyana cewa masu ruwa da tsaki da za su aiwatar da Karin albashin jami’an rundunar suna nan suna aiki kan sabon albashin har yanzu kuma za su tabbatar da faruwar hakan.

Baba ya ce wannan karin kudiri ne na shugaban kasa Muhammadu Buhari ba tare da wata bukata daga ‘yan sanda ba.

Ya kuma bayyana cewa jami’an yan sandan na sane da cewa babban tashin hankali ne a tsara duk wani abin da zai kawo cikas ga lamarin tsaro balle a aiwatar da shi, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Saura kwanaki 11 a shirya zaben shugabanni, kan jam’iyyar APC ya kara tarwatsewa

IGP ya bayyana dalilin da yasa jami’an yan sanda basu samu karin albashi ba har yanzu
IGP ya ce ana nan ana aiki kan batun karin albashin yan sanda Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

A tuna cewa a shekarar da ta gabata ne ministan harkokin ‘yan sanda, Muhammad Dingyadi ya bayyana cewa za a fara biyan sabon tsarin albashin jami’an ‘yan sanda daga watan Janairun wannan shekara ta 2022 amma tsawon watanni uku kenan ba tare da an aiwatar da shi ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Amma da yake martani ga rahotannin kafafen watsa labarai cewa jami’an rundunar na shirin yin zanga-zanga a ranar 26 ga watan Maris domin neman karin albashi da alawus dinsu, shugaban yan sandan ya bayyana cewa babu dan sandan da zai kaskantar da kansa zuwa ga yin zanga-zanga kan karin albashi saboda suna sane da illar hakan.

IGP a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mukaddashin kakakin rundunar, Muyiwa Adejobi, ya yi watsi da rahoton, yana mai cewa:

“Kokarin wasu marasa kishin kasa ne na bata sunan rundunar, da batar da al’umma da kuma zafafa harkokin siyasa.”

Kara karanta wannan

Jerin yadda Sojoji 18, yan sanda 6 da yan Najeriya 76 suka rasa rayukansu cikin mako daya

Ya ce:

“Tun daga lokacin da aka amince da hakan, hukumar albashi ta fitar da sanarwar aiwatar da hakan, mai girma ministan harkokin ‘yan sanda da kuma IGP suna nan suna ta aiki tare da hukumar FIRS domin tabbatar da dakatar da cire haraji kamar yadda Shugaban kasa da majalisar zartarwa ta tarayya suka yi umurni.”

A cewarsa, rundunar yan sandan Najeriya hukuma ce mai tsari da da’a tare da shiryayyun sharudda da ka’idoji don magance koke-koke kuma babu yajin aiki a cikin tsarin.

Shugaban ‘yan sandan ya kara da cewa:

“Ya dace a jaddada cewa IGP na kokari don ganin an aiwatar da cikakken karin albashi da alawus da shugaban kasa ya gabatar kuma majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da shi.
“Yana da mahimmanci a kara jadadda cewa shugaban kasa ne ya dauki matakin ba tare da wata bukata daga ‘yan sanda ba wajen ba da umarnin tsarin karin albashi da na alawus. Saboda haka Gwamnatin Tarayya ta jajirce sosai wajen aiwatar da sabon tsarin albashi.”

Kara karanta wannan

Kungiyar ASUU ta cigaba da yajin-aiki, za a kara wasu watanni ba a bude jami’o’i ba

Sifeto Janar IGP Alkali ya amince Mata yan sanda su fara sanya Hijabi

A wani labari na daban, Sifeto Janar na yan sanda, IGP Baba Alkali, ya amince jami'an yan sanda mata su fara sanya dan kwali mai kama da Hijabi kan kayan sarki.

Wannan ya bayyana a hotunan sanarwar da hukumar tayi kwanakin nan.

An bayyana sabon tsarin ne a ganawar IGP na manyan jami'an yan sanda ranar 3 ga Maris 2022.

Asali: Legit.ng

Online view pixel