Tashin hankali yayin da 'yan bindiga suka hallaka 'yan sanda da dama a Kebbi

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga suka hallaka 'yan sanda da dama a Kebbi

  • Labarin da ke iso mu ya bayyana cewa, an samu aukuwar wani mummunan hari a jihar Kebbi, lamarin da ya kai ga mutuwar 'yan sanda
  • An ruwaito cewa, 'yan bindiga sun kai farmaki kamfanin sarrafa tumatur da nufin sace wasu 'yan kasashen waje
  • Allah bai basu nasara ba, domin sun yi arangama da 'yan sanda kafin daga bisani suke tsere suka shiga daji

Ngaski, Kebbi - Akalla ‘yan sanda hudu ne aka kashe a lokacin da ‘yan bindiga suka kai farmaki wani kamfanin sarrafa tumatur mai suna GBFoods Africa a kauyen Gafara da ke karamar hukumar Ngaski a jihar Kebbi a ranar Talata.

An kuma kama wani mazaunin garin a wata arangama tsakanin ‘yan bindigar da jami’an tsaro, Daily Trust ta ruwaito.

Barnar 'yan bindiga a Kebbi
Tashin hankali yayin da 'yan bindiga suka hallaka 'yan sanda a jihar Kebbi | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi, DSP Nafiu Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce ‘yan bindigar sun kai kimanin 500 lokacin da suka afkawa kamfanin daga jihar Neja makwabciyarta.

Kara karanta wannan

Lawan, Goje, Amaechi Da Sauran Ƴan Siyasa 4 Da Ake Damawa Da Su Tun 1999

A cewarsa, ‘yan bindigan sun so kai hari kan ‘yan kasashen ketare a kamfanin, amma ba su yi nasara ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma ce an yiwa ‘yan bindigan ba dadi kuma sun samu raunuka, amma sun kwashe gawarwakin ‘yan uwansu nan take.

Kakakin rundunar ‘yan sandan ya ce an tura karin jami’ai a yankin, inda ya kara da cewa a yanzu haka wurin ya samu natsuwa.

A cewarsa:

“’Yan bindiga kimanin 500 sun mamaye wani kamfanin sarrafa tumatur da ke kauyen Wawu a karamar hukumar Ngaski, da nufin yin garkuwa da ‘yan kasashen waje da ke aiki a kamfanin."
"‘Yan sanda hudu sun rasa rayukansu yayin da wani farar hula kuma ya mutu a lokacin da ‘yan sanda suka kama ‘yan bindigan"

Yan bindiga sun harbe DPO, da wasu jami'an tsaro 6 a wani kazamin hari da suka kai Neja

Kara karanta wannan

Kaduna: Baya ga hari a masallaci, 'yan bindiga sun hallaka mutane, sun sace wasu mata

Akalla jami'an tsaro bakwai suka rasa rayukansu ciki har da shugaban ofishin yan sanda (DPO) na caji Ofis ɗin Nasko, ƙaramar hukumar Magama, jihar Neja, a harin yan bindiga ranar Talata.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 1:00 na rana a yau Talata, 15 ga watan Maris.

Yan bindigan sun yi yunkurin kai hari kan jam'an ƙauyen Nasko, amma jami'an tsaro da suka haɗa da yan sanda, sojoji, da yan Bijilanti suka tarbe su.

Kakakin yan sanda na jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, wanda ya tabbatar da lamarin, ya ce yan sanda biyu da yan Bijilanti hudu ne suka rasa rayukarsu a gwabzawar.

Rikici: An kaure tsakanin sojoji da wasu matasa, an hallaka mutane akalla 6

A wani labarin, rahoto daga jaridar Daily Trust ya ce, an kashe mutane hudu a yankin Obayantor da ke karamar hukumar Ikpoba Okha ta jihar Edo bayan wani rikici da ya barke tsakanin wasu matasa da jami’an sojojin Najeriya.

Kara karanta wannan

Tambuwal ya bayar da gudunmawar miliyan N30 ga iyalan yan-sa-kai da aka kashe a Kebbi

An tattaro cewa lamarin ya faru ne a ranar Juma’ar da ta gabata a cikin yankin da aka ce suna ganin rigingimun shugabanci bayan tsige shugabansu na matasa (Okhaegele) tare da nada wani sabo.

Wani mazaunin garin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya yi zargin cewa wani ne ya dauki hayar sojoji ga al’umma da nufin kwato Okhaegele, kuma a lokacin harin an kashe sojoji biyu. Ya ce daga baya sojojin suka kaddamar da harin ramuwar gayya ga al’umma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel