Tambuwal ya bayar da gudunmawar miliyan N30 ga iyalan yan-sa-kai da aka kashe a Kebbi

Tambuwal ya bayar da gudunmawar miliyan N30 ga iyalan yan-sa-kai da aka kashe a Kebbi

  • Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ya kai ziyarar ta'aziyya ga takwaransa na jihar Kebbi kan hare-haren yan bindiga
  • A yayin ziyarar, Tambuwal ya bayar da gudunmawar naira miliyan 30 ga iyalan yan-sa-kai da yan bindiga suka halaka
  • Ya kuma yi kira ga jama'a da su hadu wajen kai kokensu ga Allah domin ya kawo karshen matsalolin tsaro a arewa maso yamma da kasar baki daya

Sokoto - Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, a ranar Alhamis, 10 ga watan Maris, ya bayar da gudunmawar naira miliyan 30 ga iyalan wadanda hare-haren yan bindiga ya ritsa da su a jihar Kebbi, rahoton Daily Trust.

A ranar Litinin ne yan bindiga suka farmaki wasu yan-sa-kai inda suka kashe 65 daga cikinsu sannan a ranar Talata suka kuma halaka wasu sojoji a jihar.

Kara karanta wannan

Mataimakin Gwamnan Kebbi Ya Yi Ƙarin Haske Kan Jitar-Jitar Cewa Ya Shiga Hannun Ƴan Bindiga

Tambuwal ya bayar da gudunmawar miliyan N30 ga wadanda hare-haren yan bindiga ya ritsa da su a Kebbi
Tambuwal ya bayar da gudunmawar miliyan N30 ga wadanda hare-haren yan bindiga ya ritsa da su a Kebbi Hoto: The Sun
Asali: UGC

Tambuwal ya sanar da bayar da tallafin ne a yayin ziyarar ta’aziyya da ya kaiwa takwaransa, gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu, kan mutuwar yan-sa-kai da sojoji da aka kashe a masarautar Zuru, Daily Trust ta rahoto.

Gwamnan na jihar Sokoto ya bukaci mutanen jihar da su ci gaba da ba hukumomin tsaro hadin kai domin cimma nasara a kokarin da gwamnatocin tarayya da na jiha ke yi don magance annobar.

Ya ce:

“Mun zo nan ne domin yi wa wadanda suka rasu addu’a Allah ya jikan su sannan ya baiwa wadanda suka jikkata lafiya. Akwai kuma bukatar mu hadu muyi addu’a kan Allah ya kawo mana karshen wadannan matsaloli na tsaro a arewa maso yamma da Najeriya baki daya.”

Kara karanta wannan

Kisan Kebbi: 'Yan majalisa sun roki FG ta tura sojojin sama da kasa domin ragargazar 'yan bindiga

A martaninsa, Gwamna Abubakar Atiku Bagudu ya ce jihohin Kebbi da Sokoto dangin juna ne. ya ce:

“Mu dangin juna ne, duk abun da ya shafi daya to ya shafi dukka ne.”

Za Mu Kawo Ƙarshen Ƴan Bindiga Da Masu Kai Musu Bayanan Sirri, Tambuwal Ya Ba Mazauna Sokoto Tabbaci

A gefe guda, mun kawo a baya cewa a ranar Laraba, Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya tabbatar wa mazauna jiharsa cewa gwamnatinsa ya shirya tsaf wurin kawo karshen ‘yan bindiga da masu kai musu bayanan sirri a fadin jihar.

Har ila yau ya ja kunnen masu hada kai da su wurin tayar da hankali a jihar ko kuma su fuskanci fushin hukuma, The Punch ta ruwaito.

Tambuwal ya bayar da wannan tabbacin ne da daren Talata inda ya nuna takaicin sa akan yadda ‘yan bindiga da masu kai musu bayanai suka addabi kauyen Sabon Garin Liman da ke karamar hukumar Wurno a jihar.

Kara karanta wannan

Wani dan jarida: Irin azabar dana sha a hannun Abba Kyari bisa umarnin wani gwamna

Asali: Legit.ng

Online view pixel