Kaduna: Baya ga hari a masallaci, 'yan bindiga sun hallaka mutane, sun sace wasu mata

Kaduna: Baya ga hari a masallaci, 'yan bindiga sun hallaka mutane, sun sace wasu mata

  • Wasu 'yan bindiga sun kai mummunan farmaki wani yanki, sun hallaka mutane tare da sace wasu mata
  • Rahoto bayyana cewa, akalla mutane uku ne aka kashe a harin da 'yan bindigan suka dauki lokaci suna barna
  • Hakazalika, rahoton ya ce an sace wasu mata yayin harin, wanda aka kai a wani yankin Chikun na jihar Kaduna

Kaduna - Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a kan titin Fumigi da ke Unguwan Galadima, Gonin-Gora, cikin karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna, sun kashe mazauna tare da sace wasu mata biyu.

Mataimakin shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya reshen Arewa, Rabaran John Hayab ya tabbatar da faruwar lamarin, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kisan gillan 'yan bindiga a Kaduna
Kaduna: Baya ga hari a masallaci, 'yan bindiga sun hallaka mutane, sun sace wasu mata | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Hakan na zuwa ne kwanaki uku da sace wani limamin cocin Katolika, Rabaran Joseph Akete na cocin St. John Catholic, Kudenda da ke karamar hukumar Kaduna ta Kudu.

Kara karanta wannan

Iyalan Abacha Sun Nemi Kotu Ta Umurci El-Rufai Ya Biya Su N11.7bn Da N200m Domin Rushe Otel

Haka kuma, cikin mako guda, ‘yan bindiga sun kashe mutane biyar, tare da kona wata tankar mai a kauyen Manini, kusa da Kuriga, a kan babbar hanyar Birnin-Gwari zuwa Kaduna.

Kuriga da ke karamar hukumar Birnin-Gwari ta Kaduna, yanki ne da ya yi kauirin suna wajen yawan samun hare-haren 'yan bindiga.

Shugaban CAN, Hayab, ya ce sabon harin da aka kai a Gonin Gora ya faru ne a ranar Alhamis 10 ga watan Maris.

Ya bayyana sunayen wadanda aka kashe da Mista Aminu Bege, da dansa, da kuma wani makwabcinsa.

Hayab ya yi ikirarin cewa ‘yan bindigar sun shafe sama da sa’a guda suna baira ba tare da tsangwama ba kafin su tafi da wasu mata.

Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce a lokacin da ‘yan bindigar suka far wa jama’ar da misalin karfe 12 na rana, sun yi ta harbi ba kakkautawa.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan bindiga sun buɗe wa mutane wuta a Kaduna, rayuka sun salwanta

Ba a samu jin ta bakin jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige ba.

'Yan Bindiga Sun Sace Mutane 14 a Masallaci a Kaduna, Sun Kuma Sace Mata Da Dabobbi

An sace wasu masallata a yayin da yan bindiga suka kai hari a masallaci a ƙaramar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.

Wasu majiyoyi sun shaida wa Daily Trust cewa yan bindigan sun kai harin ne lokacin da mutanen ke sallar Ishai a ranar Alhamis.

Majiyar da ke zaune garin ya ce:

"Sun zagaye masallacin suka sace mutane 14. Sun kuma sace shanu da ba a san adadin su ba daga kauyen Tudun Amada duk a Giwa."

Daily Trust ta gano cewa yan bindigan sun dade suna kokarin kai hari a jihar amma yan sakai suna hana su shiga garin.

'Yan bindiga sun sace babban limami da wasu mutane 10 yayin da suke sallah a Sokoto

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kashe manoma 2 sannan sun yi garkuwa da wasu mutane 4 a Sokoto

A wani labarin, 'yan bindiga sun sace mutane 11 ciki har da babban limami, Aminu Garba, wanda ke shirin jagorantar mutane yin sallah Juma'a a jam'i a kauyen Gatawa da ke karamar hukumar Sabon Birni a Jihar Sokoto.

An sace limamin tare da wasu mutane uku ne a ranar Juma'a kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Maharan sun tare hanyar Sabon Birnin zuwa Gatawa a ranar Asaba, inda suka bindige mutane uku suka kuma sace wasu mutanen bakwai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel