Masarautar Katsina ta nada Sanata Ibrahim Ida a matsayin sabon Wazirin Katsina

Masarautar Katsina ta nada Sanata Ibrahim Ida a matsayin sabon Wazirin Katsina

  • An nada Sanata Ibrahim Mohammed Ida domin maye gurbin Alhaji Sani Abubakar Lugga a matsayin Wazirin Katsina
  • sakataren majalisar masarautar, Alhaji Bello Mamman Ifo, ne ya sanar da hakan a ranar Talata, 15 ga watan Maris
  • Sanata Ida ya kasance tsohon dan majalisar dokokin tarayya wanda ya wakilci yankin Katsina ta Tsakiya a majalisar dattawa tsakanin 2007-2011

Katsina - Masarautar Katsina ta nada tsohon dan majalisar dattawa, Sanata Ibrahim Mohammed Ida a matsayin sabon Wazirin Katsina.

Sashin Hausa na BBC ta rahoto cewa sarkin yakin Katsina kuma sakataren masarautar, Alhaji Bello Mamman Ifo, ne ya tabbatar mata da hakan a ranar Talata, 15 ga watan Maris.

Sanata Ida ya maye gurbin tsohon Wazirin Katsina, Alhaji Sani Abubakar Lugga, wanda ya sauka daga kujerarsa bayan takaddama tsakaninsa da majalisar masarautar.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Wasikar Mai Mala Buni ta karyata kalaman Nasir El-Rufa'i

Masarautar Katsina ta nada Sanata Ibrahim Ida a matsayin sabon Wazirin Katsina
Masarautar Katsina ta nada Sanata Ibrahim Ida a matsayin sabon Wazirin Katsina Hoto: BBC Hausa
Asali: UGC

Rahoton ya bayyana cewa kafin nadin nasa, Sanata Ida shi ne ke rike da sarautar Sardaunan Katsina.

Takaitaccen tarihin sabon Wazirin Katsina

An haifi Sanata Ida a garin Katsina a cikin shekarar 1949, ya kuma yi karatunsa na boko a gida Najeriya da Birataniya da kuma Amurka.

Sabon Wazirin na Katsina ya soma aikin gwamnati da Babban Bankin Najeriya, kuma ya rike mukamai da dama a gwamnati, ciki har da Babban Sakatare na Ma'aikatar Tsaron Najeriya.

Ya kuma wakilci yankin Katsina ta Tsakiya a majalisar dattawa tsakanin 2007-2011. Yana kuma da mata daya Hajiya Khadija da 'ya'ya da jikoki da dama.

Masarautar Katsina: Jerin yan takara 3 da ke neman kujerar Wazirin Katsina

A baya mun kawo cewa an fara hada-hadar shirya zaben maye gurni a Katsina yayin da manyan yan takara uku suka nuna ra’ayinsu na son darewa kujerar Wazirin Katsina bayan murabus da tsohon Waziri, Farfesa Sani Abubakar Lugga ya yi.

Kara karanta wannan

Tsadar man fetur: Najeriya na da mai sama da lita 1.9bn a boye, ministan Buhari

Yan takara biyu sun fito ne daga gidan Waziri Haruna kuna sune Sarkin Fadan Katsina, Abdulkadir Ismaila, dan majalisar masarautar Katsinan da kuma Abdulaziz Isa Kaita, dan Waziri Isa Kaita.

Dan takara na uku, Maliki Zayyad, kani ga marigayi Waziri Hamza Zayyad, ya kuma fito ne daga gidan Waziri Zayyana, Daily Trust ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel