Kebbi: Mataimakin gwamna ya musanta rahoton ya jagoranci sojoji sun ragargaji 'yan bindiga

Kebbi: Mataimakin gwamna ya musanta rahoton ya jagoranci sojoji sun ragargaji 'yan bindiga

  • Mataimakin gwamnan Katsina, Kanal Samaila Yombe mai ritaya, ya musanta batun cewa ya jagoranci sojoji sun ragargaji 'yan bindiga
  • Yombe ya ce yana a hanyarsa ta zuwa yankin kudancin jihar ne lokacin da ya yi kicibis da dakarun wadanda ke hanyar gudanar da wani aiki
  • Ya ce babu yadda za a yi jami'an soji masu ci su karbi umurni daga wajen wani jami'i mai ritaya

Kebbi - Mataimakin gwamnan jihar Kebbi, Kanal Samaila Yombe mai ritaya, ya yi watsi da ikirarin cewa shi ya jagoranci dakarun da suka farmaki yan bindiga wanda ya yi sanadiyar mutuwar wasu sojoji uku a yankin kudancin jihar, inda ya bayyana shi a matsayin mara tushe.

A makon da ya gabata ne yan bindiga suka kashe yan-sa-kai 65 a kauyen Makuku da ke karamar hukumar Sakaba sannan suka kashe wasu sojoji a kauyen Kanya da ke karamar hukuma Danko/Wasagu duk a jihar Kebbi.

Kara karanta wannan

Rikici: An kaure tsakanin sojoji da wasu matasa, an hallaka mutane akalla 6

Yombe, ya yi watsi da rade-radin ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Birnin Kebbi, yana al’ajabin ta yaya sojoji masu ci za su karbi umurni daga jami’i mai ritaya, Daily Trust ta rahoto.

Kebbi: Mataimakin gwamna ya musanta rahoton ya jagoranci sojoji sun ragargaji 'yan bindiga
Kebbi: Mataimakin gwamna ya musanta rahoton ya jagoranci sojoji sun ragargaji 'yan bindiga Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Ya kara da cewa ya je yankin kudancin jihar ne domin karfafa gwiwar yan gudun hijira saboda su iya komawa yankunansu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce tafiyar tasa ta yi daidai ne da na sojojin wadanda ke gudanar da aiki na daban, inda ya kara da cewar ba mai yiwuwa bane a aikin soja wani jami’i mai ritaya ya bayar da oda.

Yombe ya ci gaba da bayanin cewa yana kan tafiya ne ta wannan hanya lokacin da yan bindiga suka bude wuta kan sojojin da ayarinsa, inda ya kara da cewar an kashe daya daga cikin masu tsaron lafiyarsa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kwashe mutum 11 a Katsina bayan sojoji sun tattara komatsansu

Daily Trust ta nakalto Yombe yana cewa:

“Nima na ji wannan rade-radin cewa masu yi mani rakiya ne. Na yi karo da sojoji a kan hanyarsu ta aiwatar da wani aiki na daban, kawai mun kasance a hanya daya ne.
Sojojin ma suna bukatar karin dakaru domin aiwatar da aikin nasu. Toh, me zai sa a nemi rakiyar sojoji? Ba ni da hakkin mallakar sojoji masu rakiya. Ina da masu rakiya ta.
“Abun takaici ne wani ya bayyana cewa ni ke jagorantar dakarun sojin da ke mani rakiya. Wannan bai taba faruwa ba. Babu wanda zai yarda cewa Kanal mai ritaya na jagorantar wata runduna ta tsaro.”

Mataimakin Gwamnan Kebbi Ya Yi Ƙarin Haske Kan Jitar-Jitar Cewa Ya Shiga Hannun Ƴan Bindiga

A baya mun ji cewa Col. Samaila Yombe, mai murabus a ranar Alhamis ya musanta batun labaran da ake ta yada wa kan cewa ‘yan bindiga sun yi garkuwa da shi yayin da suka kai wa tawagarsa farmaki bayan ya kai wa sojoji ziyara a kudancin jihar.

Kara karanta wannan

Tambuwal ya bayar da gudunmawar miliyan N30 ga iyalan yan-sa-kai da aka kashe a Kebbi

Mataimakin gwamnan ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da wakilin Daily Trust a Birnin Kebbi.

Yana sahun gaba a ziyarar da ya kai wa rundunar sojin wacce ya kira da ‘Ziyarar filin dagar Sojoji’ don samun damar gane shiri da salon da sojojin suke amfani da shi wurin yakar ‘yan bindiga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel