Kun kyauta: Amurka ta taya EFCC murnar kama mai laifin da FBI ta dade tana nema

Kun kyauta: Amurka ta taya EFCC murnar kama mai laifin da FBI ta dade tana nema

  • Hukumar EFCC ta yi babban kamu, inda ta kama wani kasurgumin barawon da aka dade ana nema ruwa a jallo
  • Wannan barawo dai ana zarginsa da tafka munanan ayyukan sata da kuma zamba, wanda FBI tuna ta sanya a jerin wadanda take nema
  • Gwamnatin Amurka ta yaba wa EFCC, ta kuma EFCC murnan kama wannan kasurgumi da ya addabi jama'a

Najeriya - Gwamnatin Amurka ta taya hukumar EFCC murnar kama wani dan Najeriya da ke cikin jerin sunayen wadanda hukumar FBI ke nema ruwa a jallo bisa zarginsa da laifin zamba da ya kai dala miliyan 100, da karkatar da kudade, da kuma satar bayanan sirri.

Hukumar EFCC, a cikin wata sanarwa a ranar Litinin, ta sanar da kama mutumin, Osondu Victor Igwilo, a wani dakin taro da ke unguwar Sangotedo a Legas, a yankin Kudu-maso-Yammacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Kaduna: Baya ga hari a masallaci, 'yan bindiga sun hallaka mutane, sun sace wasu mata

Hukumar EFCC ta yi babban kamu
Kun kyauta: Amurka ta taya EFCC murnar kama mai laifin da FBI ta dade tana nema | Hoto: dailytrust.com
Asali: Facebook

Rahoton Premium Times ya ce an kama Mista Igwilo mai shekaru 42 a ranar 11 ga Maris, tare da Okafor Nnamdi Chris, Nwodu Uchenna Emmanuel da John Anazo Achukwu, kamar yadda EFCC ta bayyana.

Hukumar da ta EFCC ta ce Mista Igwilo yana cikin jerin mutanen da hukumar FBI take nam tun 2018.

Wani yankin sanarwar EFCC ya ce, ana zargin Mista Igwilo da yin satar ne ta wasu asusunan bankin kasar Amurka.

Sanarwar ta kara da cewa:

"Saboda haka, an sanya Igwilo cikin jerin sunayen FBI, biyo bayan karar da aka shigar a gaban kotun Amurka da ke Houston, Texas a watan Disambar 2016."

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta ce an kwato gidaje biyar da ke cikin yankunan Legas daga hannun Mista Igwilo.

Kara karanta wannan

'Yan Sanda Sun Gurfanar Da Tsohuwar Matar Fani-Kayode, Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama A Kotu

Hakazalika, tuni EFCC ta ce:

"Ba da jimawa ba za a gurfanar da wadanda ake zargin zuwa kotu."

Gwamnatin Amurka ta taya EFCC murnan babban kamu

Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya ya fitar da sanarwar taya murna ga EFCC nan take bayan da hukumar ta yaki da cin hanci da rashawa ta sanar da kama Mista Igwilo.

A cewar Ofishin Jakadancin na Amurka a wani sakon Twitter a ranar Litinin:

"Tare da Adalci a matsayin abin da muka sa a gaba, muna taya @officialEFCC murna bisa hada gwiwa da @FBI tare da kama Igwilo da aka dade ana nema ruwa a jallo, da laifin zamba, almundahanar kudi da kuma tafka mummunan sata."

Mu muka sace: An gurfanar da wasu mutane biyu da laifin satar taliya 'Spaghetti'

A wani labarin, an gurfanar da wasu mutane biyu Usman Yusuf mai shekaru 28 da Abdulrafiu Ashiru mai shekara 24 da ake zargin sun shiga wani shago tare da sace kwalayen taliya spaghetti na N352,000 a ranar Litinin a gaban wata kotun majistare ta Ebute Meta dake jihar Legas.

Kara karanta wannan

Yin arziki 'yan Crypto zai tabbata: Amurka ta juyo kan 'yan Crypto, za su ga canji nan kusa

Rahoton Vanguard ya ce, wadanda ake tuhumar sun bayyana ne a kan tuhume-tuhume uku da suka hada da hada baki, sata da kuma aikata laifin da zai iya kawo cikas ga zaman lafiya, kuma sun amsa laifukan da ake tuhumar su da su.

Alkalin kotun, Misis A. O. Akinde, ta bayar da umarnin tsare su a gidan gyaran hali na Ikoyi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel