Mu muka sace: An gurfanar da wasu mutane biyu da laifin satar taliya 'Spaghetti'

Mu muka sace: An gurfanar da wasu mutane biyu da laifin satar taliya 'Spaghetti'

  • An gurfanar da wasu mutane a gaban kotu a jihar Legas bisa wasu laifukan da suka shafi sata da hada baki
  • Wadanda aka kaman sun amsa laifinsu na sace kwalayen taliya spaghetti, an kuma dage ci gaba da sauraran shari'a
  • A bayanan da suka iso kotu, an bayyana yadda mutanen biyu suka shiga shagon wani tare da sace masa taliya

Legas - An gurfanar da wasu mutane biyu Usman Yusuf mai shekaru 28 da Abdulrafiu Ashiru mai shekara 24 da ake zargin sun shiga wani shago tare da sace kwalayen taliya spaghetti na N352,000 a ranar Litinin a gaban wata kotun majistare ta Ebute Meta dake jihar Legas.

Rahoton Vanguard ya ce, wadanda ake tuhumar sun bayyana ne a kan tuhume-tuhume uku da suka hada da hada baki, sata da kuma aikata laifin da zai iya kawo cikas ga zaman lafiya, kuma sun amsa laifukan da ake tuhumar su da su.

Kara karanta wannan

'Yan Sanda Sun Gurfanar Da Tsohuwar Matar Fani-Kayode, Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama A Kotu

An gurfanar da barayin taliya
Mu muka sace: An gurfanar da wasu mutane biyu da laifin satar taliya 'Spaghetti' | Hoto: punchng.com

Alkalin kotun, Misis A. O. Akinde, ta bayar da umarnin tsare su a gidan gyaran hali na Ikoyi.

Yadda suka tafka satar

Tun da farko, mai gabatar da kara, Insp Orobosa Osagiede, ya shaida wa kotun cewa wadanda ake tuhumar sun aikata laifin ne a ranar 12 ga watan Maris da karfe 3:00 na dare, a Iddo Plaza, Ebute Meta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Osagiede ya shaida wa kotun cewa, mutanen biyu sun shiga shagon wani mutum Mista Adewale Sanusi, inda suka yi awon gaba da taliya spaghetti da ya kai kudi Naira 352,000.

Laifukansu sun ci karo da sashe na 168(d), 287 da 411 na dokar laifuka ta jihar Legas, 2015.

Kotun ta dage sauraran karar har zuwa ranar 4 ga watan Afrilu domin nazarin gaskiya da kuma yiwuwar yanke hukunci.

Zamfara: 'Yan fashin daji sun fara bukatar taliya da shinkafa a maimakon kudin fansa

Kara karanta wannan

Ta Kacame: Mai Garkuwa Ya Yi Ƙorafi a Kotu, Ya Ce Abokansa Sun Cuce Shi Sun Bashi N200,000 Kacal Cikin N12m Da Suka Samu

Rufe kasuwanni masu yawa a fadin jihohin arewa maso yamma na Najeriya ya kasance babban kalubale ga 'yan fashin daji.

Daily Trust ta ruwaito cewa, a kalla gwamnonin yankin hudu ne suka umarci rufe kasuwannin jihohinsu a matsayin hanyar dakile ta'addanci.

Kwanaki kadan bayan rufe kasuwannin a wasu kayukan Sokoto, 'yan fashin daji sun fara bukatar kayan abinci a matsayin fansar wadanda ke hannunsu.

Wani mazaunin Sabon Birni, wanda ya bukaci a rufa sunan shi, ya sanar da Daily Trust yadda aka sako wata diyar makwabtansu bayan sun bada kayan abinci.

Manyan kayan abinci uku da farashin su ya yi tashin gwauron zabi a kasuwar Legas

A wani labarin, abubuwan dake faruwa a fadin duniya na cigaba da shafar kayan masarufi a Najeriya, a cewar yan kasuwa.

A wani bincike da Legit.ng ta gudanar a wata babbar kasuwa a Najeriya, mun gano cewa farashin kayan abinci bashi da tabbas kuma samun su ya kara wahala.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Bayan Kashe Ƴan Sakai 57, Ƴan Bindiga Sun Sake Kashe Sojoji 13, Ƴan Sanda 5 Da Vigilante a Kebbi

Kamar Wake, Shinkafa da Gari, farashin ya sauka da sama da kashi biyar cikin dari yayin da kayan Masarufin da ake cikin kakarsu suka kara tashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel