Obasanjo: Na bar makarantar Islamiyya ne saboda tsoron tsumagiyar Malam

Obasanjo: Na bar makarantar Islamiyya ne saboda tsoron tsumagiyar Malam

  • Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo ya sanar da cewa tsoron tsumagiyar malaman Islamiyya ce ta hana shi koyon larabci
  • Obasanjo ya sanar da hakan ne yayin bikin nada sabon khalifan Tijjaniya a Ogun inda yace yana matukar kaunar koyon ilimin Islama
  • Obasanjo mai digiri har uku a fannin ilimin addinin Kiristanci, ya ce har yau yana tuna wakokin da suka yi a baya a Islamiyya

Abeokuta, Ogun - Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a ranar Lahadi ya bada labarin yadda tsoron bulala yasa ya bar makarantar Islamiyyar da akafi sani da Ile - Kewu a kasar Yarabawa.

Duka da bulala yana daya daga cikin hukunci mai tsanani da malaman islamiyya suke amfani dashi wurin gyara dabi'ar dalibai.

Kara karanta wannan

Obasanjo: Ban Nemi Mulki Ba, Mulki Ne Ta Riƙa Bi Na A Guje

Obasanjo: Na bar makarantar Islamiyya ne saboda tsoron duka
Obasanjo: Na bar makarantar Islamiyya ne saboda tsoron duka. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Yayin jawabi a ranar Lahadi a Abeokuta dake jihar Ogun, tsohon shugaban kasar wanda ke da digiri na uku a ilimin addinin kiristanci, ya bayyana yadda yake matukar kaunar ilimin addinin Islama.

Ya bada labarin yayin rantsarwa gami da nada Sheikh Salis Alao Adenekan a matsayin babban alkalin Tijjaniyyar kasar Yarabawa, Edo da jihar Delta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Taron ya dauka hankalin shugabanni da 'yan darikar Tijjaniyyah daga dukkan jihohin kudu maso yamma, Edo da Delta, har ma da wakilin 'ya'yan Sheikh Ibrahim Nyass, daga Kaolack cikin Senegal, wanda Sheikh Abdullah Baye Ibrahim ya jagoranta.

Obasanjo, a takaitaccen tsokacin da yayi, ya bayyana wa taron addinin musuluncin yadda a matsayin su na mabiya addini, ya zama wajibi su tashi tsaye wajen neman Aljannah, wacce ita ce karshen makomar muminai.

Ya yarda cewa, duk wanda yake tunanin Aljannah a karshen makoma ba zai yi wasa da addini da ibadarshi ba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kwashe mutum 11 a Katsina bayan sojoji sun tattara komatsansu

Obasanjo ya ce, "Dalilin zuwa na nan shi ne in gaisheku. Abunda ya tattara mu nan ya shafi addini ne. Kuma daya daga cikin mahimman lamurran mu, wanda shi ne dalilin da yasa muke doron kasa don mu samu mu shiga Aljannah. Duk wanda ya san akwai Aljannah, shi ko ita ba zai yi wasa da addinin shi da ibadar shi a lokacin rayuwarsa a doron kasa ba.
"Ina godiya gare ku baki daya na karramani da taya shugaban mu a musulunci, Sheikh Adenekan murna. Ni'imar Ubangiji ta lullubeku da addinin ku."
Yayin bada labarin kaunar ilimin addinin islaman da yake yi, ya ce "A lokacin da ina yaro, na bada labarin nan ya fi a kirga, cewa Bulala ce ta hanani koyon larabci yadda ya dace. Amma duk da haka, har yanzu ina tuna wakoki da dama da muke yi a da."

Yayin gabatar da jawabinsa, fitaccen malamin addinin Islama na jihar Legas, Sheikh Suleiman Faruq Onikijiopa ya gargadi wadanda ke shugabanci a kan rashin amfani da mulki yadda ya dace, inda ya ce za a yi musu hisabi a kan abubuwan da suke aikatawa a ranar tashin alkiyama.

Kara karanta wannan

Inyamuri nike son ya zama shugaban kasa a 2023, Obasanjo

Haka zalika, Onikijipa wanda shi ne babban mai bada fatawa a Ilorin, ya ja kunnen 'yan darikar Tijjaniyyah da su cigaba da hada kawunan su don kwatarwa al'umma hakkin ta da kuma neman yancin su daga gwamnati.

A jawabinsa, gwamna Dapo Abiodun ya siffanta Ogun a matsayin "birni mai ruko da addini a Najeriya."

Abiodun, wanda shi ne shugaban ma'aikatan kasa, Shuaib Salis ya gabatar, gami da bukatar musulmai su tabbatar sun yi abunda ya dace a lokacin zaben shekarar 2023 don ganin " an zabi shugabannin da zasu kawo cigaba ga kasar."

Ya siffanta sabon babban Khalifan Tijjaniyyan da aka nada, a matsayin "mutum mai tsantseni, daraja, kima da cancantar zama jakadan addinin Islama."

Obasanjo: Kurtun Boko Haram na gaba zasu kasance daga cikin yara 14m da suka bar makaranta

A wani labari na daban, tsohon shugaban kasan Najeriya, Olusegun Obasanjo a ranar Alhamis ya koka akan yadda yaran da suka daina zuwa makaranta za su koma ‘yan kungiyar Boko Haram.

Kara karanta wannan

Jirgin kasan Legas zuwa Ibadan ya tsaya tsakiyar daji saboda mai ya kare

Obasanjo ya bayyana hakan ne yayin jawabi a wani taron gogar da matasa akan mulki a cibiyar ci gaban matasa da ke Olusegun Obasanjo Library, Abeokuta, jihar Ogun, Daily Trust ta ruwaito.

Ya yi nuni akan yadda kusan dalibai miliyan 14 suka daina zuwa makarantu su na yawo a titinan Najeriya, inda ya ce ba sai an fada wa kowa ba, ya san nan da shekaru 10 zasu zama ‘yan Boko Haram.

Asali: Legit.ng

Online view pixel