Obasanjo: Kurtun Boko Haram na gaba zasu kasance daga cikin yara 14m da suka bar makaranta

Obasanjo: Kurtun Boko Haram na gaba zasu kasance daga cikin yara 14m da suka bar makaranta

  • A ranar Alhamis tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya koka akan yadda yaran da su ka daina zuwa makaranta za su koma ‘yan Boko Haram nan babu dadewa
  • Obasanjo ya bayyana hakan ne yayin jawabi a taron gogar da matasa akan mulki a cibiyar ci gaban matasa, Olusegun Obasanjo Presidential Library, Abeokuta, jihar Ogun.
  • Ya yi nuni akan yadda yara wurin miliyan 14 suka daina zuwa makaranta su na yawo a titinan Najeriya, ya yi hasashen cewa zasu koma kungiyar Boko Haram nan da shekaru 10 masu zuwa

Ogun - Tsohon shugaban kasan Najeriya, Olusegun Obasanjo a ranar Alhamis ya koka akan yadda yaran da suka daina zuwa makaranta za su koma ‘yan kungiyar Boko Haram.

Obasanjo ya bayyana hakan ne yayin jawabi a wani taron gogar da matasa akan mulki a cibiyar ci gaban matasa da ke Olusegun Obasanjo Library, Abeokuta, jihar Ogun, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Thebo Mbeki: Yadda na yi kutun-kutun na hana Obasanjo zarcewa karo na 3

Obasanjo: Kurtun Boko Haram na gaba zasu kasance daga cikin yara 14m da suka bar makaranta
Obasanjo: Kurtun Boko Haram na gaba zasu kasance daga cikin yara 14m da suka bar makaranta. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ya yi nuni akan yadda kusan dalibai miliyan 14 suka daina zuwa makarantu su na yawo a titinan Najeriya, inda ya ce ba sai an fada wa kowa ba, ya san nan da shekaru 10 zasu zama ‘yan Boko Haram.

Obasanjo ya bayyana yadda yawan yara masu daina zuwa makaranta zai kara yawaita rashin tsaro.

A cewarsa:

“A halin da ake ciki a kasar nan muna da yara miliyan 14 da suka daina zuwa makaranta, ba sai an fada wa kowa cewa nan da shekaru 10 zuwa 14 zasu koma ‘yan Boko Haram.
“Don haka idan ba'a yi maganin Boko Haram a yanzu, nan da wasu shekaru rashin tsaro zai kara tsananta. Ta ina zamu fara? Idan batun talauci ake yi ina batun ilimi kuma?

Kara karanta wannan

Luguden wuta: Sojoji sun hallaka yan ta'adda 90, sun damke kasurgumi da suke nema ruwa a jallo

“Wani ya ce idan kowa ya samu ilimi waye zai zama bawa? "

Tsohon shugaban kasan ya jajirce akan mayar da hankali wurin hadin kan Najeriya, inda ya ce ya dinga yaki don tabbatar da hadin kai a Najeriya duk tsawon rayuwarsa, Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce, “Idan da ni shugaban yarabawa ne, da ban samu nasarori ba a kasar nan da wurin yarabawa kadai zan yi tasiri. Dan uwanmu na kudu maso gabas ya yi gaskiya, na yarda da cewa duk wani dan Najeriya ya cancanci a daraja shi.
“Kada mu yaudari kawunanmu, mutane zasu girmama mu saboda yawanmu ko kuma yawan tsintsiya babu shara ne? Kullum idan na fita kasashen waje ana sukar mu kuma ba laifinsu bane.
“Ban taba da na sanin yaki don samar da hadin kai a kasar Najeriya ba. Kuma ko yanzu bukatar hakan ta taso zan jajirce akai. Amma a halin yanzu yakin neman shugabancin na kwarai ake yi.”

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna ga PDP: Ku bar tikitin shugaban kasa a zaben 2023 ga mai rabo

Thebo Mbeki: Yadda na yi kutun-kutun na hana Obasanjo zarcewa karo na 3

A wani labari na daban, bincike ya ci gaba da bayyana yadda burin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo na mulkar Najeriya a karo na uku ya ki tabbata, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Tsohon shugaban kasan Afirka ta kudu, Thabo Mbeki ya bayyana yadda shi da tsohon shugaban kasan Najeriya, Abdulsalami Abubakar suka hada kai wurin hana Obasanjo zarcewa karo na 3.

Obasanjo ya dade ya na musanta zama cikin wadanda suka bukaci gyara a kundin tsarin mulkin Najeriya wanda zai amince ya mulki Najeriya a karo na uku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel