Obasanjo: Ban Nemi Mulki Ba, Mulki Ne Ta Riƙa Bi Na A Guje

Obasanjo: Ban Nemi Mulki Ba, Mulki Ne Ta Riƙa Bi Na A Guje

  • Cif Olusegun Obasanjo, tsohon shugaban kasar Najeriya ya ce shi a rayuwarsa gudun mulki ya ke yi amma mulkin kuma tana binsa a guje
  • Obasanjo ya furta hakan ne yayin wata jawabi da ya yi wurin taron Keggites Club of Nigeria da aka shirya don bikin cikarsa shekaru 85.
  • Ya bada misalan lokuta da dama da aka nemi ya karbi mulki amma ya ki yarda har dai sai lokacin da ya zama ba mafita sannan ya karba

Abeokuta, Ogun - Tsohon shugaban kasar Najeriya, Chief Olusegun Aremu Obasanjo ya bayyana cewa 'bai nemi mulki ba, mulkin ne ta rika binsa.'

Obasanjo ya yi magana ne a Abeokuta, yayin da ya ke martani kan wasu batutuwa da ake tattaunawa, wurin taron kungiyar Keggites Club of Nigeria ta hannun Unity in Diversity Forum.

Kara karanta wannan

Lawan, Goje, Amaechi Da Sauran Ƴan Siyasa 4 Da Ake Damawa Da Su Tun 1999

Lakcar, wacce aka yi a dakin taro na dakin karatu ta Obasanjo, wani sashi na cikin bikin cikarsa tsohon shugaban shekaru 85 a duniya, rahoton Vanguard.

Obasanjo: Ban Nemi Mulki Ba, Mulki Ne Ta Riƙa Bi Na A Guje
Obasanjo: Ban Nemi Mulki Ba, Mulki Ne Ta Riƙa Nema Na. Hoto: Vanguard
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wurin taron, Dr Yemi Faroumbi, Dr Festus Adedayo da Farfesa Kolawole Kazeem sun gabatar da kasidu a wurin taron.

Kalaman na tsohon shugaban kasar, amsa ce ga tsohon jakadan Najeriya a Philiphines, Dr Yemi Farounbi, wanda ya yaba wa Obasanjo a matsayin mutumin da bai taba neman mulki ba, Vangaurd ta rahoto.

Farounbi, a kasidarsa ya ce, Obasanjo ya ki amincewa da kirar da aka masa ya zama shugaban kasa na mulkin soja a 1976, bayan juyin mulkin da ta yi sanadin rasuwar Janar Murtala Muhammed da wasu sojoji.

Ya ce, "Shi (Obasanjo) ya zama shugaban mulkin soja ne ba domin yana so ba. Na samu bayanin abin da ya faru a ranar 13 ga watan Fabrairun 1976 daga bakin Janar T.Y Danjuma da wasu daban."

Kara karanta wannan

Iyalan Abacha Sun Nemi Kotu Ta Umurci El-Rufai Ya Biya Su N11.7bn Da N200m Domin Rushe Otel

"Na kuma san ya yi iya kokarinsa wurin kin amincewa ya zama dan takarar jam'iyyar PDP sai daga baya ya zama shugaban kasa a zaben 1999."
"Zan iya tabbatar da hakan domin har da ni a lokacin. Ba ya da ra'ayin neman mulki, amma mulki ke nemansa saboda irin tarbiya da halayensa."
"Tambar Annabi Dauda ya ke a Bibul, wanda ba ya son zama sarki, amma yana da halayen sarki. Ya nuna jarumta wurin kashe zaki da hannunsa."

Martanin Obasanjo kan lakcar

Da ya ke martani kan lakcar, Obasanjo, wanda ke cike da farin ciki bisa abin da lakcarorin suka fadi, ya gasgata kalaman Farounbi.

Ya ce, "A wani lokaci kai (Farounbi), ka ce bana son yin mulkin siyasa. Horaswar soja aka bani. Daya daga cikin horaswar shine ba ruwan soja da siyasa kuma hakan ta yi tasiri a kai na."
"Amma kamar yadda ka ce, duk da cewa na rika kokarin raba aikin soja da siyasa, mulki ya rika bi na kuma ina gudu, na cigaba da gudu har lokacin da ta kai ba zan iya kauracewa mulkin ba."

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban majalisar wakilan tarayyar da ya rika karbar albashin N15, 000 ya rasu

Tsohon shugaban kasar ya yi kira ga yan kungiyar su cigaba da hada kansu wuri daya yana mai cewa hadin kansu na cikin abin da ya ke bukata domin zama uban kungiyar.

2023: Ƙungiyar musulmai ta buƙaci Gwamna Ugwuanyi ya fito ya nemi kujerar Buhari

A wani rahoton, kungiyar hadin kan al’ummar musulmi, UMUL ta bukaci dan kabilar Ibo ya tsaya takarar shugaban kasa idan 2023 ta zo, The Sun ta ruwaito.

Kungiyar ta musulmai ta ce lokaci ya yi da cikin yankuna biyar da ke kasar nan, ko wanne yanki zai samu adalci da daidaito da juna, hakan yasa take goyon bayan Igbo ya amshi mulkin Najeriya.

Kamar yadda kungiyar ta shaida, dama akwai manyan yaruka uku a Najeriya, Hausa, Yoruba da Ibo, don haka in har ana son adalci, ya kamata a ba Ibo damar mulkar kasa don kwantar da tarzomar da ke tasowa.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Tsohon dan wasan kwallon Najeriya ya yanki jiki ya fadi matacce a Jos

Asali: Legit.ng

Online view pixel