Jirgin kasan Legas zuwa Ibadan ya tsaya tsakiyar daji saboda mai ya kare

Jirgin kasan Legas zuwa Ibadan ya tsaya tsakiyar daji saboda mai ya kare

  • Mai ya karewa sabon jirgin kasan Legas zuwa Ibadan da shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar kwanaki
  • Fasinjoji sun fito daga cikin jirgin da ya tsaya a tsakiyar daji suna kokarin ganewa idanunsu abinda ya faru
  • Yan Najeriya a kafafen ra'ayi sada zumunta sun tofa albarkatun bakinsu kan wannan lamari

Legas - Jirgin kasa mai jigilar fasinjojo daga jihar Legas zuwa Ibadan, a ranar Alhamis, ya tsaya tsakiyar dajin sakamakon karewar mai a cikinsa.

Wani ma'abocin manhajar Tuwita, @shollychei ya saki bidiyon yadda fasinjoji suka fito daga cikin jirgin don ganin ikon Allah.

Yayinda wasu fasinjojin sun zauna kan layin dogon, saura na hira a tsaye.

Amma daya baya ya dawo yace jirgin ya tashi, zasu cigaba da tafiya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Lawan, Goje, Amaechi Da Sauran Ƴan Siyasa 4 Da Ake Damawa Da Su Tun 1999

Wannan abu ya auku yayinda yan Najeriya ke fama da tsadar man fetur a fadin tarayya.

Birane irinsu Legas, Abuja, Fatakwal da ire-irensu sun jijjigu da dogayen layukan mai wanda ya kai ga har kwana ake a gidajen mai.

Ga lokacin da ake zuba mai;

Martanin yan Najeriya:

Abubakar Fana Aminu:

Kai wani abin, almara sai kasata Nigeria Ubangiji Allah ya kawomana shuwagabanni masu jin tausayimmu ameen ya Rabbi

Umar Aliyu:

Du da matsalar tsaron da yake damin mu amma jubi wani abin kunya wai jirgin gwamnati babu mai a cikin sa

Zakari D Bocho:

Babbar magana karamci Mai harda jirgin kasa a Nigeria Allah ya kiyaye gaba Kar ace Mai yakarewa jirgin Buhari a sararin samaniya, manja zezama ja kenan

Aliyu Suleiman:

Wannan ai sakaci da ganganci yakamata a hukunta duk wanda suka jawo wannan sakacin don kiyaye rayuka da dukiyoyin al'umma.

Kara karanta wannan

Indiya ta maye gurbin Najeriya matsayin hedkwatar talauci na duniya

Jibrin Usman Bakori:

Subar shege nan kawai su kama gaban su, idan kuma za su iya su tura shi zuwa gari wajen ƴanbunburutu a zuba.

Bashir Muhammad Tagana:

Wannan ba dai dai ne ba,
Wasane da rayukan Al'umma, yadda qasar nan ya dagule ga harakar tsaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel