'Yan Sanda Sun Ceto Matar Da Fusatattun Matasa Ke Zargi Ta Kashe Mijinta Saboda Naci Wurin Kwanciyar Aure

'Yan Sanda Sun Ceto Matar Da Fusatattun Matasa Ke Zargi Ta Kashe Mijinta Saboda Naci Wurin Kwanciyar Aure

  • Yan sandan Jihar Anambra sun ceto wata mata da aka gani a wani bidiyo da ya bazu fusatattun matasa na ci mata mutunci
  • Fusatattun matasan sun zargi matar ne wacce ba a bayyana sunanta ba da kashe mijinta saboda naci a wurin kwanciyar aure
  • Rundunar yan sandan ta bakin kwamishina CP Echeng Echeng ta tabbatar da sahihancin bidiyo tare da kama mutum daya cikin wadanda ake zargin

Anambra - Rundunar yan sandan Najeriya reshen Jihar Anambra ta ceto wata mata da kawo yanzu ba a bayyana sunanta ba daga hannun fusatattun matasa a garin Aguleri a jihar a ranar Asabar.

Yan uwan marigayin mijin suna zargin matar ne da kashe mijin ta saboda matsa masa da naci wurin kwanciyar aure.

Yan sanda sun ceto matar da ake zargin ta kashe mijinta saboda naci wurin kwanciyar aure daga fusatattun matas
Yan sanda sun ceto matar da ake zargin ta kashe mijinta saboda naci wurin kwanciyar aure daga fusatattun matasa. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

A wani bidiyo da ya karade dandalin sada zumunta, an hangi matar babu tufafi zaune a gefen gawar mijinta yayin da mutanen unguwa ke mata tsawa.

Kara karanta wannan

Ta hadu da bacin rana: An kama wata gurguwar karya tana bara, an tursasa ta yin tafiya a bidiyo

Yan sandan sun tabbatar da sahihancin bidiyon ga wakilin The Punch a ranar Lahadi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mun kama jagoran wadanda suka ciwa matar mutunci, muna fadada bincike - Yan Sanda

Jami'an tsaron sun kuma ce an kama wanda ake zargin shine jagoran wadanda suka ci mutuncin matar.

Kakakin yan sanda, Tochukwu Ikenga, ya ce:

"Rundunar yan sandan Anambra a yau 12/2/2022, ta ceto wata mata daga hannun fusatatun mutane a Aguleri.
"An ceto ta ne sakamakon bidiyon da ya karade gari inda aka nuna matar a fili ana ci mata mutunci kan zargin ita ta yi sanadin mutuwar mijinta.
"Kwamishinan yan sanda, CP Echeng Echeng, yayin Allah wadai da abin da aka yi mata, ya ce an kama wanda ake zargi sannan ya umurci a bincike bidiyon da nufin gano sauran wadanda ake zargin don a hukunta su."

Kara karanta wannan

Karfin Hali: Hotunan motar da barayi suka fasa a farfajiyar kotu, sun sace kudade

Sanarwar ta kuma ce an gano an birne mamacin kafin bidiyon ya fara yawa a kafafen sada zumunta. Matar yanzu haka tana asibiti ana kula wa da ita.

Wani mutum mai shekaru 42 ya mutu suna tsakar 'gwangwajewa' da budurwarsa a ɗakin otel

A wani labarin daban, 'yan sanda a birnin Nairobi na bincike kan wani lamari da ya faru a kasar inda wani mutum mai shekaru 42 ya yanke jiki ya fadi yayin lalata da budurwarsa, LIB ta ruwaito.

An rahoto cewa Erastus Madzomba ya rasu ne a daren ranar Laraba 29 ga watan Disamba, yayin da ya ke gwangwajewa da budurwarsa mai suna Elgar Namusia a otel din Broadway Lodgings a Kawangware.

Rahoton da yan sanda suka fitar ya nuna cewa satin su biyu da fara soyayya.

Rahoton ya kara da cewa:

"Jami'an yan sanda sun garzaya zuwa inda abin ya faru suka tarar da gawar wanda abin ya faru da shi yana kwance a cikin dakin da aka ambata."

Kara karanta wannan

Kaduna: Bayan karbe kudin fansa, 'yan bindiga sun sheke wanda suka sace

Asali: Legit.ng

Online view pixel