Ta hadu da bacin rana: An kama wata gurguwar karya tana bara, an tursasa ta yin tafiya a bidiyo

Ta hadu da bacin rana: An kama wata gurguwar karya tana bara, an tursasa ta yin tafiya a bidiyo

  • Dubun wata matashiyar yarinya da ke karyar gurgunta tare da zama kan keken guragu ya cika a jihar Lagas
  • Mutane sun cika da mamaki bayan da aka tilsatawa yarinyar ta tashi tsaye daga kan keken guragun kuma ya bayyana karara cewa ba gurguwa bace
  • An tilasta mata yin tafiya sannan mutanen da ke wajen suka dunga tunani kan yawan kudin da ta tara a wannan harka

Jama’a sun tofa albarkacin bakunansu bayan bayyanar wani bidiyo na wata mabaraciya da ta yi ikirarin cewa ita gurguwa ce don kawai ta tara kudi a daga harkar bara.

Yarinyar na zama ne a kan keken guragu wanda musamman ta tanade shi domin yin wannan harka da kuma yawo a yankin Ikeja tana rokon kudi daga hannun mutane a matsayin mai nakasa.

Kara karanta wannan

Daga rubutu a Twitter: An daure 'yar jarida saboda yiwa shugaban kasa gugar zana

Ta hadu da bacin rana: An kama wata gurguwar karya tana bara, an tursasa ta yin tafiya a bidiyo
An tilasta mata yin tafiya Hoto: @elnukstudio
Asali: Instagram

An tilasta mata yin tafiya

Lokacin da wasu matasa da suke lura da ita suka kama ta, sai suka tilasta mata sauka daga keken guragun sannan suka sa ta yin tafiya. Tana sauka, sai ya bayyana karara cewa duka kafafuwanta guda biyu lafiya suke babu abun da ya same su.

Don haka mutane da dama sun bayyana cewa bara tamkar kasuwanci ne a gare ta. Shafin @instablog9ja ya wallafa bidiyon da aka dauka na yarinyar.

Kalli bidiyon a kasa:

Mabiya shafukan zumunta sun tofa albarkacin bakunansu

@wendy_adamma ta ce:

"Irin wadannan mutanen na da yawa a nan Lagas. Kowa neman na kai yake yi dan Allah."

@michelledera ta yi martani:

"Asiri ya tonu" duk mun cika da mamaki."

@callmedamy ta yi martani:

"Kasuwa ta baci fa."

Kara karanta wannan

Gudun tsira: Mutune sun mutu garin gudun tsira a wani kauyen Katsina

@opsyswagger ta yi martani:

"Na daina basu kudi lokacin da na gane cewa yawancinsu na amfani da dabaru iri-iri don rokon kudi."

@iambiggysteve ya yi martani:

"Wannan ta batawa ainahin guragu kasuwa."

An kama wata mabaraciya da kudi har N500,000 da dala 100 a Abuja, an tsare ta

A wani labarin kuma, mun ji cewa an kwamushe wata mabaraciya mai suna Hadiza Ibrahim a Abuja dauke da kudi N500,000 da kuma dala 100.

Jaridar Punch ta rahoto cewa mazauna yankin sun shiga rudani bayan da aka samu matar dauke da wadannan makudan kudade.

Kakakin hukumar kula da harkoki, zamantakewa da ci gaban babban birnin tarayya, Shaka Sunday, ya tabbatar da cewar matar na tsare a hannun hukumar a yankin Bwari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng