Karfin Hali: Hotunan motar da barayi suka fasa a farfajiyar kotu, sun sace kudade

Karfin Hali: Hotunan motar da barayi suka fasa a farfajiyar kotu, sun sace kudade

  • Wata mata 'yar Najeriya ta ja kunnen mutane a kan hatsarin barin kudi a cikin motoci, inda ta bada labarin abunda ya faru da wani makusancin ta
  • Matar ta bayyana yadda mai motar ya aje ta a kofar shiga wata kotu, kafin ya dawo, barayi sun balle motar gami da yin awon gaba da kudaden shi.
  • Hotunan motar da aka wallafa a yanar gizo na nuna tarwatsatstsun windunan motar don samun damar aukawa cikin ta, duk da ba'a bayyana yawan kudin da aka sace ba

An tabo gidan adalci cikin kwanakin nan, yayin da barayi suka samu damar aukawa wata motar da aka ajiye a kusa da harabar wata kotu, inda su ka yi awon gaba da wasu kudade.

Kara karanta wannan

Karuwai sun yi wa direbo yajin aikin mako 1 kan cin zarafin abokiyar aikinsu da aka yi

Bayan wallafa hotunan aukuwar lamarin a kafar sada zumuntar Facebook, ya nuna yadda aka tarwatsa windunan motar da ballalun gilasai a kujerun motar.

Karfin Hali: Hotunan motar da barayi suka fasa a farfajiyar kotu, sun sace kudade
Karfin Hali: Hotunan motar da barayi suka fasa a farfajiyar kotu, sun sace kudade. Hoto daga Ebeyin Ikpi Eyong
Asali: Facebook
"Hakan zai iya taimakon wani. Mutane ku yi hattara da barin kudi cikin mota, hakan na da hatsari. An aje motar nan ne gaban kofar wata kotu, daidai kofar shiga ofishin kotun, kafin mai motar ya dawo cikin mintoci kadan, wasu hatsabibai sun rusa mishi mota, gami da kwashe mishi makudan kudi."

Ga wallafar:

Jama'a sun yi martani

Ga wasu daga cikin tsokacin masu amfani a kafafan sada zumuntar zamani:

Prince Maurice Edem ya ce: "Tabbas bin bayan shi suka yi.. Al'umma na fama da rashin 'yan canji yanzu. Karancin kudi da karancin wahala."
Grace Asuquo tayi martani da: "Ban ji dadin hakan ba, babu tsaro a Calabar."

Kara karanta wannan

Yin arziki 'yan Crypto zai tabbata: Amurka ta juyo kan 'yan Crypto, za su ga canji nan kusa

Eunice Ekpo yayi tsokaci: "Ba zan karyata ki ba, saboda hakan ya faru da mahaifina."
Ugbe Bright Agoinim ta ce: "Wannan ya dade yana faruwa sama da shekaru da dama, ya faru da mijina wasu shekaru da suka shude. Na samu labarin yadda suke aukawa bankuna. Ku yi hattara da yawan kudaden da kuke yawo da su."

A kan bashin N2.7m da ta ke bin sa, magidanci ya nada wa matarsa mai juna biyu dukan mutuwa

A wani labari na daban, ana zargin wani MC dan Najeriya mai suna Bonus Emmanuel Chigozie, da yi wa matarsa mai juna biyu, Itunu Lawal Emmanuel mugun dukan da yayi ajalinta.

Mummunan lamarin ya auku a gidansu da ke yankin Okota a jihar Legas kamar yadda shafin Instablog9ja ya ruwaito.

Kamar yadda wata majiya ta sanar, "Sun yi aure shekaru hudu da suka gabata. Emmanuel ya fara dukan matarsa bayan sun yi haihuwar farko. Kwatsam ya zamo ya tsane ta kuma a kodayaushe neman dalilin da zai ci zarafinta yake yi."

Kara karanta wannan

Hotuna da bidiyon ranar bakin ciki ga Abba Kyari yayin da ya bayyana a gaban kotu

Asali: Legit.ng

Online view pixel